Fitaccen Ɗan Wasa Kun Aguero Zai Daina Buga ƙwallon Kafa A Sakamakon Ciwon Zuciya Da Yake Damun Sa - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Fitaccen Ɗan Wasa Kun Aguero Zai Daina Buga ƙwallon Kafa A Sakamakon Ciwon Zuciya Da Yake Damun Sa

Fitaccen Ɗan Wasa Kun Aguero Zai Daina Buga ƙwallon Kafa A Sakamakon Ciwon Zuciya Da Yake Damun Sa
Fitaccen Ɗan Wasa Kun Aguero Zai Daina Buga ƙwallon Kafa A Sakamakon Ciwon Zuciya Da Yake Damun Sa



Fitaccen ɗan wasan ƙasar Argentina kuma wanda a yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Bacerlona ta ƙasar spaniya kun Aguero. Wata majiya na nuna cewa akwai yiwar ɗan wasan zai daina taka leda gabaki ɗaya.


Fabrizio Romano wanda fitaccen ɗan jarida ne a fagen wasannin tamola shine ya fitar da wannan rahoton inda ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafin sa na sada zumunta na twitter a ranar Asabar. Kuma duk mai bibiyar harkar kwallo yasan cewa indai labari ya fito daga wajen Fabrizio to na gaskiya ne domin ba ya wallafa labaran ƙarya.


Fabrizio ya rawaito wannan labarin ne daga wajen ɗan jaridar ƙwallon ƙafa a Sipaniya Gerrard Romero cewa ɗan wasa Aguero zai ajiye takalmansa daga buga ƙwallo gabaki ɗaya sakamakon wasu matsaloli na rashin lafiya da suka danganci ciwon zuciya wanda ake ganin cewa cigaba da buga ƙwallo zai zame masa illa da barazana ga rayuwar sa.


Aguero dai yana da shekaru 33 kuma ya shafe tsawon lokaci yana taka leda a manyan ƙungiyoyi dake nahiyar Turai wanda kuma ake ganin ya kusa yin ritaya. Shi dai Aguero ya lashe manyan kofi na  tun a tsohuwar ƙungiyar sa ta Manchester city dake ƙasar England. 

Related Posts:

Ana tunanin cewa a taron da manema labarai na mako mai zuwa da ƙungiyar Bacerlona za ta yi za ta sanar da halin da ake ciki game da makomar ɗan wasan dangane da ritayar sa daga buga tamola wanda hakan babbar barazana ce ga ita kanta ƙungiyar ta Bacerlona.

 
Aguero dai ance ya shafe kusan shekaru 18 ya na taka leda a manyan ƙungiyoyin nahiyar Turai kamar su Atletico Madrid, Manchester city da kuma Bacerlona. Aguero dai yafi daɗe a ƙungiyar Manchester city inda ya shafe tsawon lokaci kafin ya koma Bacerlona. Kuma a ƙungiyar ya ɗauki koguna da dama.


Bacerlona dai ta ɗauko ɗan wasan ne domin ya maye gurbin ɗan wasa Lionel Messi wanda ya bar ƙungiyar ya koma PSG dake ƙasar Faransa. Suna ganin cewa zuwan Aguero din zai cike gurbin ɗan wasa Lionel Messi sai dai kuma gashi alamu sun nuna cewa hakan ba zai samu ba.


Dama dai tun zuwan Aguero Bacerlona yake fama da rauni wanda sai da ya ɗauki tsawon lokaci kafin ya warware ya fara take leda. Sai dai kuma tun bayan fara buga wasanni ya fara samun matsalar ciwon zuciya wanda ke neman tilasta masa ajiye takalmansa gabaki ɗaya.


Yanzu dai abin jira agani shine ko wane ɗan wasa ne Bacerlona za ta ɗauko da zai iya maye mata gurbin wannan ɗan wasa Aguero da ya kamu da ciwon zuciya, amma ana ta danganta ɗan wasa Erlin Harland na ƙungiyar Dortmund da cewa zai zo Bacerlona. Lokaci ne dai zai tabbatar da hakan.

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel