Fitaccen Mawaƙi Davido Ya Bada Tallafin Miliyan 250 Ga Gidajen Marayu A Najeriya
Fitaccen Mawaƙi Davido Ya Bada Tallafin Miliyan 250 Ga Gidajen Marayu A Najeriya |
Shahararren mawaƙi a Najeriya da nahiyar Afirka David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya cika alƙawarin sa da yai na bada tallafin kuɗi ga gidajen marayu 292 har Naira miliyan 250. Davido yayi wannan alƙawarin ne tun a shekarar 2021, wanda kuma sai a wannan lokacin ne ya cika wannan alƙawarin.
A shekarar 2021 ne dai mawaƙi Davido zai raba kuɗi har Naira miliyan 250 ga gidajen da marasa galihu a faɗin ƙasa baki ɗaya. Davido yace yayi hakan ne domin murnar zagayowar ranar da aka haife shi. Ya bayyana hakan ne a shafin sa na Instagram a ranar Talata.
Mawaƙin ya bayar da cikakken bayani tare da bayyana sunayen gidajen marayun da suka amfana da kuɗaɗen da ya bayar, inda yace gidajen marayu kimanin 292 ne suka amfana da tallafin nasa. Haka kuma mawaƙin ya yabawa ƴan kwamitin da ya kafa domin tabbatar da cewa saƙon yaje inda ake so.
Yace kwamitin na ɗauke da mutane jajirtattu da suka iya gudanar da aiki. Domin su ma sun bada gudunmawa sosai wajen tabbatar da cewa saƙon ya isa guraren da aka ware.Daga ƙarshe kuma mawaƙin ya yabawa magoya bayansa da danginsa da kuma abokan sa baki ɗaya bisa irin kulawa da tallafin da yake samu daga garesu.
Tun a 2021 mawaƙin yai wata sanarwa a cikin shafin sa na Instagram cewa zai yi bikin ranar haihuwar sa, don haka yana so yaga abinda magoya bayansa za su bashi, wanda hakan yasa masoya daga sassa daban-daban suka ringa tura masa da kuɗi ta account ɗin sa.
Wanda cikin lokaci kaɗan ya tara maƙudan kuɗi. Sai dai daga baya ya sanar da cewa zai raba kuɗin ga gidajen marayu a faɗin Najeriya a matsayin tallafi ga gidajen marayu wanda kuma tun a lokacin akai ta tsare-tsaren yadda za'a raba kuɗin, sai gashi kuma zuwa yanzu an kammala yin hakan.
Irin hakan dai ba kasafai aka saba ganin hakan na faruwa ba, domin ba'a saba ganin mawaƙa a Najeriya suna yin irin wannan tallafin ga gidajen marayu ba. Wannan ne yasa jama'a ke ta yabawa mawaƙin bisa irin wannan jinƙai da mawaƙin ya nuna.
Leave Comments
Post a Comment