Duk Rashin Ƙarfinka Wajen Gamsar Da Iyalinka Ga Wani Abu Da Zaka Ringa Shafawa A Gabanka Idan Zakai Jima'i —Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Duk Rashin Ƙarfinka Wajen Gamsar Da Iyalinka Ga Wani Abu Da Zaka Ringa Shafawa A Gabanka Idan Zakai Jima'i —Android Pols

Duk Rashin Ƙarfinka Wajen Gamsar Da Iyalinka Ga Wani Abu Da Zaka Ringa Shafawa A Gabanka Idan Zakai Jima'i
Duk Rashin Ƙarfinka Wajen Gamsar Da Iyalinka Ga Wani Abu Da Zaka Ringa Shafawa A Gabanka Idan Zakai Jima'i


An gaisheku maza, yau shirin naku ne. Game da gyara gida, ance idan an gyara mata suma maza a gyara su. Maza da yawa suna yi mana ƙorafin cewa ba ma kawo musu nasu gudunmawa sai mata kawai. To ba wai ba ma san baku bane abinda yasa muka fi karkata wajen mata don su sunfi buƙatar yin gyara ne kuma duk abubuwan da suke yi suna yi ne domin ku mazan. To amma dai yau kuma maza mun zo muku da wani sirri da za kuyi amfani dashi domin ku gyara zamantakewar ku da matan ku.


Idan gaban mutum ƙarami ne a dabi'a ta halitta, to kasani cewa duk wani magani da za'a ce za'a baka domin ta ƙara girma babu wani girma da za ta yi sai dai a baka ka yi amfani da abubuwan da zai sa ta ƙara yin ƙwari, kuma ta ƙara yin kuzari ta yadda za ta iya biyan buƙata ba tare da an samu matsala ba. Amma mu ba wata ƙwaya za mu ce kuyi amfani da ita ba. Mai ne da za kuyi amfani dashi a duk lokacin da za ka yi saduwar aure sai ka yi amfani dashi ka shafa a gananka. Idan kuma ba jima'i za ayi ba to ba'a yin amfani dashi.


Abubuwa 2 za ku yi wannan haɗin da su, za ku nemi gwanda, nasan dai babu wanda zai ce bai san ta ba. Idan ka same ta sai ka yanka ta wannan ƙwallayen na cikin ta su ake da buƙata za ka kwashe su a markaɗa su blander, idan kuma babu sai ku sami ƙaramin turmi irin na ƙarfe ku daka wannan ƙwallayen a ciki. Idan kun daka ko kun markaɗa sai ku samu wani mazubi mai kyau ku zuba a ciki. Sai ku ɗauko man Kaɗanya ku zuba kamar cokali 1 a cikin wannan markadaɗɗen ƙwallon da kuka daka.


Ku samu roba ko kwalba mai murfi ku zuba a ciki saboda gudun kada ya lalace ko kuma ya zube. A duk lokacin da zaka sadu da iyalin ka sai ka ɗauko wannan haɗin ka shafa a gabanka. Shima wannan haɗin yana da matuƙar tasiri ga duk wanda yake yin amfani dashi. Domin duk tsufanka, duk yadda gabanka ya kai da rashin miƙewa, duk rashin kuzarin ka, duk rashin ƙarfin ka da kasa gamsar da iyalin ka ka jarraba yin amfani da wannan man kasha mamaki.


Kamar yadda muka sha yin bayani cewa duk waɗannan abubuwan muna kawo muku su ne kyauta sabdoa Allah, kuma muna yi ne domin masu aure waɗanda suke da matsala don su samu su warware wannan matsalar. Sai dai idan kasan ba kada aure kada ka yi amfani da abubuwan da muke bayarwa domin ba munyi ne domin marasa aure ba. Munyi ne domin maza masu mata ko kuma mata masu maza. Da fatan za'a kiyaye.


Kada ku manta ƙwallayen gwanda za'a samu sai ku daka shi ko kuma ku markaɗa shi sannan ku samu mai na Kaɗanya ku haɗa ku cakuɗa ku ringa shafa shi a gaban ku a duk lokacin da za ku kusanci Iyalin ku. Zaku shafe duka gaban naku dashi. Shi man Kaɗanya yawancin masu sayar da kayan gargajiya suna sayar dashi, cokali biyu ya isheku kuyi amfani dashi.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel