Duk Namijin Da Baya Iya Yin Minti 30 Tare Da Iyalinsa Ya Yi Amfani Da Wannan |
Ga duk mutumin da yakeso ya ɗauki dogon zango yana tare da iyalinsa ba tare da ya sauka da wuri ba. Wanda yakeso ya daɗe yana yin jima'i da matar sa wato saduwar aure ba tare da ya yi inzali ba, wato ba tare da ya kawo ba. Domin akwai maza da suke yawan ƙorafin cewa ba sa iya yin dogon zango suna yin mu'amalar aure da iyalan su. Shiyasa yau muka ce za mu taimaka muku domin Ganin kun samu biyan buƙata.
Amma sai dai shi wannan haɗin ba zai maka amfani ba idan kanada cutar ciwon siga, basir da kuma ciwon sanyi. Saboda idan kana da ɗaya daga cikin su ba za su bari wannan haɗin yaima aiki ba. Don haka anan ina kira gare ku maza da ku nemi maganin basir da sanyi domin waɗannan cutuka ba ƙaramin kashe namiji suke ba. Idan a baya kana yin kuzari kana gasmar da iyalinka yanzu kuma sai kaji baka iya yin hakan to kodai matsalar basir ne ko kuma cutar sanyi sai kuyi maganin su, akwai shirye-shiryen mu da suka gabata da mukai bayani akan yadda za'a yi maganin sanyi da kuma basira.
Idan kunyi maganin basir da sanyi sai kuyi wannan haɗin. Kuma wallahi aikin da wannan haɗin keyi a jikin mutum babu adadi sai dai kawai mu faɗa muku waɗanda muka sani. Namijin Goro zaku samu, za kuji muna yawan kawo muku abubuwa wanda ake haɗawa da namijin goro ayi amfani dasu. To shi dai namijin goro aikin da yake yi ba zai lissafu ba domin yanayin aiki tare da magance cutuka masu yawan gaske a jikin ɗan adam. Shiyasa muke kawo muku wasu daga cikin abinda muka sani game da namijin goro.
Duk namijin da iyalinsa suka raina shi a dalilin kasa yin kuzari a yayin da yake tare da ita. Ya samu namijin goro yaci idan ya rage baifi minti 30 ko 40 ba zai kusanci matar sa ba. Ka samu guda ɗaya ko biyu manya ka tauna ka cince ka tsotse ruwan. Hanya ta biyu kuma zaka iya yayyanka shi ka busar dashi kasa a daka shi ya zama gari. Idan ya rage baifi saura awa 1 ka kusanci iyalin ka ba ka samu ruwan shayi da Lipton ka zuba wannan garin kamar cokali 2 ka shanye.
Idan akwai zuma zaka iya haɗawa da ita kasha, idan kuma babu to ba dole ne ba ka sha a haka. Daga ranar idan baka yin minti 10 to sai kadawo kanayin minti 30 ba tare da ka gaji ko ka yi inzali ba. Wallahi duk namijin da zai yi wannan haɗin yasha to ba zai ƙara samun matsala da iyalinsa ba. Kai idan matarka ma mai alheri ce ranar har kyauta sai ta yi maka sabdoa irin yadda ka gamsar da ita. Domin dama su mata babban burin su mijin su ya gamsar dasu da jima'i, duk namijin da baya iya yin hakan to matarsa raina shi takeyi.
Sai dai shi wannan haɗin mun bayar dashi ne saboda maza masu aure wanda suke da matsalar rashin daɗewa suna jima'i. Idan kasan bakada aure karkayi wannan haɗin domin ba na marasa aure bane idan kuwa kayi to kaida Allah ba mu yafe ba.