Domin Matan Aure: Yadda Za Ku Yi Maganin Ƙaiƙayin Gaba, Buɗewar Gaba Da Ƙurajen Gaba |
Mata masu matsalar Ƙaiƙayin gaba, buɗewar gaba, ƙurajen gaba da fitar farin ruwa mai wari wanda ke damun mata da yawa. To indai wannan matsala ce yau na zo muku da wani sabon haɗi na musamman wanda duk wacce ta yi shi to za ta rabu da wannan matsala da muka ambata tun a farko.
Mata na cikin gida ku riƙe wannan sirrin. Ku ringa haɗawa kuna dafa shi kuna sayarwa da ƴan uwan ku mata. Hakan zai taimaka wajen gyra jikin su, kema kuma zaki samu kuɗin shiga. Uwargida ko amarya ku yi ƙoƙarin haɗa wannan sirrin domin zai amfane ku sosai.
Domin Matan Aure: Yadda Za Ku Yi Maganin Ƙaiƙayin Gaba, Buɗewar Gaba Da Ƙurajen Gaba
Shi wannan haɗin ba shi da wata wuyar haɗawa kuma abubuwan da zaki haɗin da su ba su da wuyar samu, ga abubuwan da zaki samu kamar haka;
(1) Ganyen Lalle ko kuma Garin lalle, duk wanda kika samu za ki iya yin amfani da shi.
(2) Ganyen Magarya, shima kamar na farkon kodai garin sa ko kuma ganyen duka wanda aka samu ya wadatar.
(3) Kaninfari
Yadda zaki shine idan kin haɗa waɗannan abubuwan da muka lissafa guda 3 a sama sai ki ɗebi garin lalle kamar cokali 2, shi kuma garin Magarya cokali 1 shi kuma kaninfari kamar rabin cokali zaki ɗiba. Sai ki zuba su a cikin tukunya ki zuba ruwa babban kofi 2 zuwa 3 ki tafasa shi.
Idan ya tafasa sai ki sauke shi ki bari ya ɗan huce sai ki juye shi a cikin bawo ko roba mai ɗan faɗi sai ki ɗauko Miski ki ɗiga kaɗan a ciki sannan ki zauna a ciki na tsawon minti 20. Haka zaki ringa yin wannan haɗin a kowace rana ko kuma duk bayan kwana 2 har tsawon wata 1.
Kada kiyi sake da wannan haɗin domin idan kinyi za kiji daɗin sa sosai. Sannan kuma kiyi ƙoƙari ki sanar wa da ƙawayen ki da abokiyar zaman ki domin su ma su amfana daga wannan sirrin. Allah yasa a dace amin.