DALILAN DA SUKE KAWO CIWON ASTHMA
DALILAN DA SUKE KAWO CIWON ASTHMA |
Akwai abubuwa da dama dake kawo ciwon asthma, zan lissafo su kamar haka;
Daga cikin abubuwan da ke kawo ciwon Asthma sun hada da :-
-Genetic wato mutum yayi gadon cutar daga wuri iyayensa ko kuma makusanta.
-Respiratory infection :- Ga wadanda suke da wani ciwon daban shima da ya shafi matsalar numfashi, kamuwa da ciwon Asthma zai iya kasancewa abu mai sauqi garesu.
-Environment Allergens, Yanayin muhallin da mutum yake rayuwa a ciki na iya sawa ya kamu da larurar Asthma, musamman masu maqwbtaka da manyan kamfanunnuka da suke fitar da gurbatacciyar iska.
- Smoking
Ma'abota shan sigari da masu yawan shan iskar da take da hayaqi zasu iya kamuwa da ciwon Asthma.
-Occupational Exposure
Yanayin sana'ah shima na daga cikin abunda ke iya sawa mutum ya gamu da larurar Asthma musamman masu ta'amalli da chemical ko hayaqi a wurin sana'ar su.
-Emotional factor
Shi wannan baya saka ciwon Asthma amma yana tsananta ta ga wanda yake da larurar Asthma misali Bacin rai, Baqin ciki, Dariyar da take kaiwa matakin da mutum sai ya qware.
-Strenuous Exercise, Aikin qarfi ko motsa jiki mai tsananin wahala.
Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad
RN,RM,PND
Leave Comments
Post a Comment