Cutar Hanta: A Kalla Mutane Miliyan Daya Ke Mutuwa Duk Shekara A Duniya — Bincike - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Cutar Hanta: A Kalla Mutane Miliyan Daya Ke Mutuwa Duk Shekara A Duniya — Bincike

Cutar Hanta: A Kalla Mutane Miliyan Daya Ke Mutuwa Duk Shekara A Duniya
Ciwon hanta


Cutar Hanta: A Kalla Mutane Miliyan Daya Ke Mutuwa Duk Shekara A Duniya. A Bikicen Shekarar 2015.


Bincike ya nuna cewa akwai abubuwan dake janyowa dan adam cutar hanta wadda a turance ake kiranta da Hepatitis da hanyoyin da za abi don a magance ta da yadda za’a baiwa jiki garkuwa. Bugu da kari, cewon ya kasu iri-iri da hanyoyin dake janyowa a kamu data dda da alamominta. Ire-iren cutar biyar sune, Hepatitis A, Hepatitis B, Hepatitis C, Hepatitis D, Hepatitis E, inda kuma daga cikin wannan ire-iren, akwai masu bacewa da kansu, inda kuma wasunsu sai anyi magani. 


Har ila yau, wasunsu basa Tsananta, inda kuma wasunsu suna tsanantawa amma bincike ya nuna cewa, cutar Hepatitis A, Hepatitis B, da Kuma Hepatitis C sune suka fi wanzuwa tsakanin bil adama. Kamar yadda binciken ya sanar, cutttukan hanta suna da yawa bawai cutar bace kadai ke lakata hantar wanda ya kamau da cutar ba akwai sauran cututtuka da dama dake lalata hanta ko yi mata wani lahani wadanda au ana gadon su ne daga gun iyaye ko kuma ya danganta ne daidai da gwargwadon ahekarau dan adama. Cutar tana janyo mutuwar zuciyar wanda a kamu da ita da lalacewar kodar sa da rufe masa hanyar dake daukar jini daga hanta zuwa zuciyar wanda ya kamu da kuma lalacewar huhu ga masu yin tu’amalli da shan taba sigari da sauran su.


Yadda ake daukar jini daga hanta zuwa zuciya Kamar yanda bincike ya nuna a Shekarar 2015 akalla yan adama miliyan 114 ne ke dauke da cutar “Hepatitis A” a fadin duniya, inda kuma kalla bil adama su miliyan 343 ne ke dauke da “Hepatitis B”. Har ila yau, a kalla mutane miliyan 142 ke dauke da “Hepatitis C” a fadin duniya, inda kuma a kalla bil adama su miliyan daya ke rasuwa a duk shekara a fadin duniya. Bugu da kari, bincike ya nuna cewa, a kasar Amurka akalla mutane 250,000 ne ke kamuwa da wannan cuta a duk shekara, yayinda akalla mutane 75 ke rasuwa a duk shekara sanadiyar Hepatitis.


Almomin Cutar Hanta 


Hepatitis A:- ciwon ciki, Zafin Jiki, Amai, Tashin Zuciya, Kasala, Bakin Fitsari, Idanuwa da Fata su koma rawaya-rawaya da sauransu, inda ita irin wannan nau’in na cutar, bata tsananta in an kamu da ita.


Hepatitis B:– Zafin Jiki, Kasala, Idanuwa zasu yi yalo da fata da Idanuwa, Gudawa da Kuma wasu alamomin masu kama da Cutar murar tsintsaye kuma wannan nau’in na cutar, wani lokacin bata nuna alama haka, tana iya tsananta da kashi 10 cikin dari na mutanen da suka kamu da ita.


Ita kuwa, Hepatitis C:- Iri daya ce da Hepatitis B, amma wannan tana iya tsananta da kashi 75 zuwa kashi 80 cikin dari na wanda ya kamau da ita. Tsawon kwanaki daga lokacin shigarta jikin wanda ya kamu har zuwa bayyananar lamominta:


Hepatitis A:- Daga sati biyu zuwa Sati Bakwai ita kuwa cutar Hepatitis B, daga sati shida zuwa sati ashirin da uku, inda kuma cutar Hepatitis C daga sati biyu zuwa sati biyu ko zuwa sati ashirin da biyar.


Abubuwan dake haddasa cutar hanta 


Hepatitis A:- abinda ke haddasata shi ne wani kwayar cuta da mai ido baya iya gani, tunda ita kuma cutar Hepatitis B, Hepatitis B Birus (HBB) haka ita kuma cutar Hepatitis C:- Hepatitis C Birus (HCB). Har ila yau, yawan tu’ammali da barasa da gubar dake fita da matsalar garkuwar jiki da yin amfani da kwayoyin magani bisa Bisa ka’ida ba ana kuma yin gado da sauransu. Hanyoyin kamuwa da cutar: Hepatitis A:- Gurbatuwar abinci ko ruwan sha da ya gurbata da sauransu.


Cutar Hepatitis B:- idan aka sanyawa mutum jinin mai dauke da ita da yin amfani da allura ko Reza dake dauke da kwayar cutar daga Uwa zuwa Danta da lokacin yin jima’I a tsakanin mace da namiji dake dauke da cutar da sauransu.


Hepatitis C:- Sanyawa mutum jinin mai dauke da ita da yin amfani da allura Ko Reza mai dauke da kwayar cutar da musayar abubuwan tsafta wanda mutum daya ya kamata ya yi amfani dashi da sauransu.


YADDA AKE GANO CUTAR A JIKIN DAN ADAM


Ana Iya Gano Cutar Hepatitis (ciwon Hanta) Ne A Jikin Mutum Bayan Alamunta Sun Fara Bayyana, Daga Nan Sai Ayi Gwajin Jini Biyo Bayan Zukar Jinin Mutum.


Yadda ake magance ciwon hanta


Zuwa asibiti mafi kusa don saduwa da ma’aikacin lafiya idan mutum ya fara jin alamun ta da aka zayyyana a sama.


Hadurran dake tattare da wanda ya kamu da ita: Babban hatsarin shi ne, Hantar wanda ya kamu da cutar zata iya lalacewa ta yanda dole sai dai ayinmasa dashen wata idan kuma da tsautsayi ya gitta, zai iya mutuwa.


Yadda ake kare jiki daga kanuwa da cutar:


Ana iya kare ta hanyar yin allurar rigakafi, inda kuma akwai maganin da ake cewa Hepatitis Baccine wata allurar ce. Ana kuma yiwa mutum ne da zarar an haifeshi, inda kuma a sati na shida dana goma dana goma sha hudu da haihuwar Jariri, inda za a yi allurar a dunkule. Ana kuma son a dinga kula da gyaran muhalli, musamman don kaucewa daga kamuwa da cutar ta hanta.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel