Crypto da Tattalin Arzikin Kasashe, Yadda Nijeriya Zata Amfana 2 - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Crypto da Tattalin Arzikin Kasashe, Yadda Nijeriya Zata Amfana 2

Crypto da Tattalin Arzikin Kasashe, Yadda Kasarmu Nijeriya Zata Amfana
Crypto da Tattalin Arzikin Kasashe, Yadda Kasarmu Nijeriya Zata Amfana 


Kafin mu chigaba da bayani, bari muyi duba akan rubutunmu na baya, sannan mu alaqan tashi da ya da kasarmu Nijeriya zata amfana da makamanchin wayancan tsare-tsare ta fuskar tattalin arzikinta.


Nijeriya ta kasance chikin kasashen da akafi yin cryptocurrency aduniya, kuma ta kasance achikin kasashen da al'ummarsu sukafi rungumar crypto aduniya (adoption). Nijeriya ta kasance wata babbar kasuwa a duniya crypto, har takai cewa duk kasuwar crypto ko wani crypto project da yan Nijeriya suka runguma, to tabbas zai karbu a Africa dama sauran kasashe. Kusan dukkan manya da kananun kasuwannin crypto suna aiki a Nijeriya, ammafa kasancewar babu tsari daga gwamnati yana kawo chuta sosai daga kasuwannin crypto ga yan Nijeriya. Rashin tsarinmu yasa kasuwannin crypto suka dora kowanne kalar token akansu, duk rashin inganchinsu. Da yawan kasashen da suke da yawan yan crypto a duniya sunyi tsarin da ba kowanne kalar token ake dorawa a kasuwannin su ba. Misali, a kasar Indiya wacce ake gani tana kan gaba wajen yawa da kuma saurin karbar crypto ga yan kasarta, sunada exchange tasu ta kashin kansu, wato WazirX wacce itace babbar exchange a Indiya. Dukda cewa Binance, Paxful, Koinex, Zebpay, da sauransu suna aiki a kasar Indiya amma fa ba'a barsu kara zube suna chin karensu babu babbaka ba kamar yanda yake a Nijeriya, a'a ansa musu ka'idoji da dolene su bisu.


Misali, a kasashen America, Indiya, da sauransu sunyi tsarin cewa duk wani dan kasarsu da yayi rijista da kasuwar crypto, dolene wannan kasuwar ta tura bayanansa ga gwamnati. Tamkar dai bankine da muke amfani da BVN wajen budewa, dukkan bayananmu CBN tana dasu. Hikimar hakan shine magance matsalolin tsaro, damfara, sata da sauransu. Misali, mun sani cewa ana amfani da kudin crypto wajen sayen abubuwan kayan laifi, tunda idan ta banki za'a tura kudin dolene gwamnati tasan da cewa za'a tura saboda yawansu, kuma dolene tabi ba'asi domin sanin me za'ayi da kudin idan sunje. Bayanda za'ayi kaje banki ka tura 300M Naira zuwa wani a kasar waje ba tareda banki sun sanarda hukuma ba kafin a basu damar tura kudin, watakila sai EFCC da/ko ICPC sun shigo chiki domin jin ba'asin me za'ayi da kudin. Ammafa da crypto, sai a sayi 2 BTC kawai a tura, wanda kudin 2 BTC ya haura 300M Naira, kuma chikin kankanin lokachi kudin sunjewa wanda aka turawa, kuma kome za'a saya dasu na laifi za'a saya ba tareda gwamnati ta sani ba. Amma idan aka hada kai da kasuwannin crypto, to suma zasu kasance tamkar banki. Ma'ana, akwai adadin yawan kudin da za'a tura da exchange dole sai sun sanar da gwamnati kafin su tura. Misali, idan gwamnati ta fadawa exchanges cewa duk kudin daya haura $50k a sanar da gwamnati kafin a tura, shikenan idan mutum zai tura 1 BTC sai an fara sanarda gwamnati tabi ba'asi kafin a tura, domin kuwa kudin 1 BTC ya haura $50k.


Ta fuskar haraji, Nijeriya tana chikin kasashen da ake hada-hadar miliyoyin daruruwan daloli a crypto, musamman akan OTC trade da shine akafi hada-hadar manyan kudade wanda gwamnati batada sanin ma anayinsa. Idan har gwamnati zata hada kai da kasuwannin crypto ba karamin kudade zata dinga samu ba amatsayin haraji daga garesu. Misali, a OTC trade ba'a trade da kasa da $10k, to koda 0.05% kawai gwamnati take karba na wannan kudaden, Allah ne kawai yasan dubu daruruwan daloli da zatana karba a OTC kawai. Kuma akwai sauran bangarori barkatai da gwamnati zatana samun kudin shiga idan ta hada kai da kasuwannin crypto. 


Zan chigaba...


Sunusi Danjuma Ali 

Web3 Advocate II Founder, SCTv Africa


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel