Crypto da Tattalin Arzikin Kasashe, Yadda Kasarmu Nijeriya Zata Amfana - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Crypto da Tattalin Arzikin Kasashe, Yadda Kasarmu Nijeriya Zata Amfana

Crypto da Tattalin Arzikin Kasashe, Yadda Kasarmu Nijeriya Zata Amfana
Crypto da Tattalin Arzikin Kasashe, Yadda Kasarmu Nijeriya Zata Amfana 


America itace kasar da tafi kowacce kasa morar crypto a duniya. Crypto ya taimakawa America wajen habbakar tattalin arzikinsu sosai, hakan kuma yasa kasar ta America ta zama gatan crypto a duniya. America ta dokantar da crypto a kasarta tamkar yanda ake dokantar da bankuna a kasashen duniya, ta yanda duk wata kasuwar crypto da take aiki a kasar America saita yadda da tsarin dokokin da America ta kebancewa crypto. Haka abin yake akan dubunnan coins da tokens da ake dasu a duniyar crypto. Duk wani crypto da za'ayi trading dinsa a America, sai an bawa kwararru sun tantanceshi, sai anyi masa rijista a hukuma a America,  sannan sai masu token din sun saka hannun akan wayancan kebantattun dokokin crypto na America. Hakane ma yasa wasu daga chikin kasuwannin crypto da suke aiki a kasar America saida saida suka samar da platform na yan America kadai. Misali, kasuwar Binance tana app daban da suka warewa yan kasar America, don haka Binance da muke amfani da ita a Nijeriya da sauran kasashe, ta banbanta da Binance da ake amfani da ita a America. Binance ta America ba kowanne coin ko token ake samu achikinta ba, sai iya wayanda suka chika ka'idojin America. Hakane ma idan zamu sayi wasu tokens musamman akan Dex, sai suce mana wannan tokens din ba'a trading dinsa a kasar America. Hatta Worldcoin da muke claiming duk wata, zamuga suna gargadinmu cewa ba'a trading dinsa a America.


USDT, USDC, DAI, FDUSD, TUSD, da sauransu dukkansu stablecoins ne da akayi pegging dinsu da American Dollar. Ma'ana, anyi musu tsarin da kowanne lokachi zasu kasance daidai da darajar Dollar ta zahiri da muke gani. Wannan stablecoins da ake amfani dasu a duniya sunyi matukar taimakawa Dollar America wajen kara mata daraja, domin kuwa suna taimakawa Dollar ta zahiri yin karanchi a duniya, kuma hakan yake sawa kullum chikin nemanta ake aduniya, kuma dai mun sani duk abinda ake bukatarsa amma kuma yayi karanchin samu dolene yayi daraja.


Yanda tsarin stablecoin yake shine, ba'a kirkirar stablecoin ayi pegging dinsa da kudin wata kasar dole saida yardar kasar. Dukkan stablecoins dana lissafa a sama ba'a kirkiresu ba saida yarda kasar America. Yanda tsarin yake shine, aduk adadin stablecoin da akayi minting akan blockchain, dolene kamfanin wannan stablecoin coin din ya nemo kudin zahiri (na takarda) ya kai wannan kasar ya ajiye a babban bankinsu (central bank). Misali, aduk 1 USDC da akayi minting akan blockchain, dolene kamfanin Circle (kamfanin Circle shine mamallakin USDC stablecoin) ya nemi Dollar ta zahiri yakai American Central Bank ya ajiye. Yanzu haka akwai 48.07B USDC da yake yawo a kasuwannin crypto wanda akayi minting gaba daya (source: CoinGecko), don haka dolene kamfanin Circle ya ajiye 48.07B Dollar ta zahiri a babban bankin America. Idan kuma kamfanin Circle zasu kara minting 1M USDC, dolene sai sun fara nemo $1M ta takarda sunkai babban bankin America kafin abasu dama. Haka zalika idan kamfanin Circle yana son rage yawan USDC da take yawo a kasuwannin crypto, saiya turasu a burning address, sannan yaje babban bankin America ya amshi kudadensa daidai da adadin USDC daya rage a kasuwa.


Zanchi gaba....


Sunusi Danjuma Ali

Web3 Advocate II Founder, SCTv Africa


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel