Buhari Ya Nemi Afuwar Ƴan Najeriya Dangane Da Matsalar Wutar Lantarki Da Man Fetur Da Ake Fama Dashi A Faɗin ƙasar
Buhari Ya Nemi Afuwar Ƴan Najeriya Dangane Da Matsalar Wutar Lantarki Da Man Fetur Da Ake Fama Dashi A Faɗin ƙasar |
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana kaɗuwar sa akan irin halin da al'ummar ƙasar ke ciki na matsalar ƙarancin man fetur da wutar lantarki wanda ya shafi ko wane ɓangare a faɗin ƙasar. Shugaban ya nuna damuwar sa kan halin da suke ciki a yanzu.
Sanarwar ta fito ne a ranar Laraba ta hannun mai taimakawa shugaban ƙasa kan yaɗa labarai Garba Shehu. Inda Buhari ya bayyana takaicin sa da nuna damuwar sa akan yanayin da al'umma suke ciki. Ya ce za su duk abinda ya dace wajen magance matsalolin.
Shugaban ya tabbatar wa da al'ummar ƙasar cewa nan ba da jimawa ba za'a shawo kan matsalar ƙarancin man fetur da wutar lantarki da suka addabi al'umma a dukkanin faɗin ƙasar. Inda yace cikin lokaci kaɗan matsalar za ta zama tarihi.
Ya ce suna sane da irin wahalar man fetur da al'umma suke ciki da sauran abubuwa da suka dangance shi wanda kuma a sanadin haka ya haifar da matsalar ƙarancin wutar lantarki, haka kuma ya kawo naƙasu ga rayuwar al'umma, amma a cikin lokaci kaɗan matsalar za'a magance ta, a cewar sa.
Ina mai amfani da wannan dama domin baiwa ƴan ƙasa kowa da kowa haƙuri kan halin da aka samu kai a ciki, ayi haƙuri nan ba da jimawa ba za muyi maganin matsalar. Don gwamnati na yin aiki tuƙuru ba dare ba rana wajen ganin an magance matsalar man fetur ɗin da kuma wutar lantarki, kuma komai zai warware, inji Shugaban Ƙasar.
Tun a farkon watan Fabrairu ne dai aka fara samun matsalolin man fetur a faɗin Najeriya inda ake cewa an shigo da wani gurɓataccen man fetur cikin ƙasar wanda yai sanadin lalacewar ababan hawa da yawa a faɗin ƙasar. Sai dai kuma daga baya gwamnatin tarayya ta ce za'a ɗauki mataki akan wanda suke da hannun akan wannan al'amari.
Amma kuma tun bayan nan ne dai ake ta samun matsalar ƙarancin man fetur ɗin a faɗin ƙasar, wanda ya haɗa da dangogin sa kamar kalanzir, iskar gas da sauran su. Wanda hakan ya jawo hauhawar farashin man da dangogin sa, a sakamakon hakan ne kuma aka samu karuwar tashin kayan masarufi da sauran abubuwan amfani na jama'a.
Leave Comments
Post a Comment