Birnin Mina Saudiya — Android Pols
![]() |
Birnin Mina Saudiya |
Mina (da Larabci : مِنَى , Minā ), wanda ake yi wa lakabi da "Birnin Tantuna, wani kwari ne mai tazarar kilomita 8 kudu maso gabashin birnin Makka, a gundumar Masha'er, lardin Makkah a yankin Hijaz na Saudiyya.
Mina ta fi shahara a lokacin aikin Hajji ("Hajji"). Domin saukar da mahajjatan da suke kwana a Mina a cikin watan Zul-Hijjah. Ana kafa tantuna fiye da 100,000 masu na'urar sanyaya daki a yankin, wanda ya ba Mina lakabin "Birnin Tantuna." Mina zata iya daukar mahajjata miliyan 3 a lokaci guda, Mina an kira shi babban birnin duniya (saboda kabilu da al'ummai daban-daban na duniya dake ziyartarta). Jamarat (Wajen Jifan Shaidan) guda uku, wadanda ke cikin kwarin Mina, su ne wurin da ake yin Jamarat (Jifa), a tsakanin fitowar rana da faduwarta a kwanakin karshe na aikin Hajji. Jifan Shaidan dai na tunawa ne da jifan shedan da Annabi Ibrahim (AS) ya yi, wanda ya so hana shi aiwatar da umurnin Allah na ya yanka dansa Annabi Isma'il (AS).
Tarihi
A sunnar Musulunci, Ibrahim (AS) ya bar matarsa Hajar (Hajara) da jaririnsu Annabi Isma’il (AS) a kwarin Makka. A wata ziyara da ya kai da iyalansa a Makka, Allah ya umarce shi a mafarki da ya yanka dansa Annabi Isma'il (AS) a Mina. Yayin da yake shirin gudanar da hadayar dan nasa, Shaidan (Iblis) ya nemi ya hana shi, sai Allah ya umarce shi da ya jefi Shaidan. Sunnar Jamarat (Jifa) ita ce tunawa da wannan imani na Annabi Ibrahim (AS), kuma an yi imanin cewa Mina ita ce wurin da Ansar (Mutanen Madina) sukayiwa Annabi Muhammad (SAWW) mubaya'a a Al-Aqabah.
Wani lokaci a cikin shekarun 1990s, gwamnatin Saudiyya ta kafa tantunan yaduka na dindindin a Mina. Wadannan tantunan yaduka sun yi gobara, wanda ya yi sanadiyar rayukan alhazai da dama. Bayan gobarar Mina a shekarar 1997 wadda ta yi sanadin mutuwar mahajjata sama da 340, an gina tantuna sama da 100,000 na dindindin, kuma ba masu fuskantar hadarin gobara ba.
Leave Comments
Post a Comment