BAYANI AKAN CIWON KANSA NA NONO (BREAST CANCER)
BAYANI AKAN CIWON KANSA NA NONO (BREAST CANCER) |
Ciwon daji na Nono (breast cancer) yana faruwa ne lokacin da wani sauyi da ake kira maye gurbi (mutations)ya faru a cikin kwayoyin halittar da ke daidaita girman kwayar halitta.
Maye gurbi (mutations) yana barin kwayoyi(cell) su rarrabuwa kuma su ninka ta hanya mara sarrafuwa.
Cancer ta nono kansa ce da ke faruwa a cikin ƙwayoyin nono,yawanci ciwon daji yana samuwa a cikin lobules ko ducts na nono.
Lobules sune gland(bututu) dake samar da ruwan Nono, ducts kuma sune hanyoyin dake kawo madara daga gland(bututu) zuwa bakin nono. Ciwon daji kuma na iya faruwa a cikin nama mai kitse ko nama a cikin nono.
A farkon matakin ciwon nono bazai haifar da wata alama ba yawancin lokuta, ciwace-ciwacen daji na iya zama ƙanana da ba zaa iya ji ba, amma har yanzu ana iya ganin rashin daidaituwa akan mammogram (magwajin cutar)
Idan ana iya jin kumburi, alamar farko yawanci sabon kululu ne a cikin Nono da babu shi a can baya,duk da haka ba kowanne kululu bane yake nufin akwai ciwon daji na nono
Kowane kalar ciwon daji na nono yana iya haifar da alamu iri-iri,yawancin waÉ—annan alamun suna kama da juna, amma wasu na iya bambanta.
Alamomin cutar sankarar nono da aka fi sani sun haÉ—a da
1. Fatar nono tayi ja,sannan Nonon ya rika yin zafi idan aka taba shi ko haka kawai.
2. Jin radadi a cikin Nonon
3. Fitar jini daga kan Nono.
5. Fitar ruwa kamar Nono wanda kuma shi ba Nono bane
6. Kumburi ko jin zafi a kasan hannu.
7. Ganin sauyi a kalar fatar Nono.
Ganin wani daga cikin alamomin nan ba shine zai iya tabbatar da kina dauke da cancer Nono ba,misali jin zafi a Nono yakan faru lokacin da wani kurji zai fito a wajen wanda ba cancer ba.
Rabe-Raben Ciwon Cancer Nono.
1. Triple-negative breast cancer
2. Metastatic breast cancer
3. Inflammatory breast cancer.
Sannan cutar cancer tana da matakai har guda hudu.
Dr. A. Z
Leave Comments
Post a Comment