An kashe tsohon Firayim Ministan Kongo Patrice Lumumba 1961
![]() |
An kashe tsohon Firayim Ministan Kongo Patrice Lumumba 1961 |
A Rana Mai Kamar Ta Yau 17 Ga Watan Junairu 1961 Aka kashe tsohon Firayim Ministan Kongo Patrice Lumumba.
PATRICE LUMUMBA DAN SIYASAR KASAR CONGO
Sunan Patrice Hemery Lumumba daya ne daga cikin sunayen da ba za a taba mantawa da su ba a tarihin Afrika, musamman tarihin Kongo Dimokradiyya, domin ya rayu cikin kunci da takura ne saboda kasar Kongo ta samu cikakken ‘yanci cikin karama da daraja, shi ne mutumin da Jifara ya sifanta da cewa “Shahidin juyin juya hali na duniya”, inda ya kalubalanci zalunci ‘yan mulkin mallaka..
Shugaban kasar Misira Jamal Abdul Nasir ya rubuta wa takwararsa na Ghana Kwami Nkurma wasikar ta’aziyyar Patrice Hemery Lumumba, yana nuna damuwarsa da kisar gillar da aka yi masa, yana cewa: Na kwana cikin bakin ciki da damuwa, ina mai jin wata kuna a cikin zuciyata a duk sanda na tuna cewa akwai sojojinmu a can cikin sojojin majalisar dInkin duniya, wannan ya nuna cewa ‘yancin da muka tafi karewa ne aka saita aka harba da makaminmu.. Shin wane ne Patrice Hemery Lumumba da wadannan jiga-jigan gwarazan Afrika suka yi ta’aziyyar rasuwarsa da wadannan kalmomi?
An haifi a 1925, a wani kauye da ake kira ”Katana Kurokombi” a yankin “Kasai”, ya fara karatunsa ne a daya daga cikin makarantun mishan, sannan daga baya ya shiga makarantar horas da ma’aikatan gida waya a garin Liyoboldfil”, yana dan shekaru 19 ya fara aiki a gidan waya a garin “Sitanlifil”. Lallai a wannan lokacin ne ya rayu cikin mafi munin yanayin wariyar launin fata tsakanin mazauna Turawa da ‘yan asalin wurin wato Bakake, a kuma nan ne ya gina zuciyarsa akan kishin kasa.
Ya jagoranci samar da yarjejeniya ta kiyaye hakkoki tsakanin kabilun Afrika, ya kuma yi aiki tukuru wajen samar da hadin kai a tsakani, a cikin wannan yanayin ne ya karanci ilimin dokoki da ilimin tsimi da tanadi, ya kuma yi kos-kos masu yawa domin karfafa kansa da kansa a ilmance.. Sai dai ashe idanuwan ‘yan mulkin mallaka ba su kauce ga barinsa ba, sai da suka kirkira masa tuhumar aikata laifin sata, da kuma haka suka sami daman jefa shi gidan yari, bayan ya fito ne ya yi iya abin da zai iya wajen daukan nauyin iyalansa.
A shekarar 1958 ne Patrice Lumumba ya shiga aikin siyasa ka’in –da- na’in, taron da aka yi a “Akra” a Disamba, 1958 shi ne taron share fage domin kafa kungiya hadin kan Afrika, a kuma wannan dandamali ne sunansa ya yi cara, bayan nan ne ya kafa jam’iyyarsa ta siyasa (MNC), bayan masu fada a ji a kasar sun amince wa ‘yan kasa da su kafa jam’iyyun siyasa, da farko ‘yan mulkin mallakar Beljika sun yi burin su zabo wa mutanen Kongo mutanen da za su mulke su ne, mutanen da suke za su cigaba da kiyaye maslahar Beljika, amma Patrice Lumumba ya ce ina?! Ya kafa jam’iyyarsa inda a cikin manyan manufofinta akwai cikakken samun ‘yanci, ba ‘yancin je ka na yi ka ba, ya kuma tuntubi duk inda ya dace a ciki da wajen kasarsa domin nema wa wannan jam’iyya goyon baya.
A shekara 1959 ‘yan mulkin mallaka sun kama shi suka sanya shi a gida yari, yana ciki aka gudanar da zabe, sai dai abin mamaki jam’iyyarsa ce ta lashe mafi yawan kujerun da aka yi takara akansu.
Patrice Hemery Lumumba ya zama farkon Fira-minista na kongo a ranar 21 ga watan Yuni, 1960.
Ya jagoranci wannan sabuwar hukuma har na tsawon watanni 8, yana mai kokarin gina kasar Kongo, kwatsam sai wani dan tawaye da ya taso karkashin kulawar ‘yan mulkin mallaka wato Muwais Tshumbi ya bayar da sanarwar ballewar wani yanki daga cikin kasar, wato yankin Katanga mai arzikin ma’adinai, a kuma shekarar ce ya fara yaki da hukumar Lumumba, bayan ya sami taimakon sojojin haya daga kasar Beljika..
A ranar 17 ga watan Junairu, 1961 kwatsam sai aka ga gawar Lumumba da wasu daga cikin makusantansa, an kuma ga wata takarda tana dauke da wasicin Lumumba zuwa ga ‘ya’yansa da matarsa tana cewa: “Ya ku ‘ya’ya na, ku tafi Misra, za ku tafi wajen Babanku Jamal ne”.
Leave Comments
Post a Comment