An Kashe Shugaban Ƙungiyar ISWAP A Wani Hari Da Rundunar Soji Suka Kai Musu A Jiragen Yaƙi
Monday, January 20, 2025
0
An Kashe Shugaban Ƙungiyar ISWAP A Wani Hari Da Rundunar Soji Suka Kai Musu A Jiragen Yaƙi |
Jiragen na Super Tucano da sauran jiragen rundunar sojin sama ta NAF suka haɗa kai inda suka kai hari ga maɓoƴar mayaƙan na ISWAP dake a yankin Marte wanda biyo bayan luguden wuta da akaiwa mayaƙan yai sanadiyyar mutuwar Shuwaram tare da sauran mayaƙan.
Wata majiya tace kafin rasuwar sa Sani Shuwaram ya samu raunuka a jikin sa masu yawa wanda ba zai iya tashi ba a sakamakon ruwan wuta da jiragen sojin suka yi musu wanda daga bisani kuma aka tabbatar da cewa Shuwaram ɗin ya mutu.
Jim kaɗan bayan Kashe shugaban na ISWAP ƙungiyar ta ba da sanarwar naɗin sabon shugaba mai suna Bako George a matsayin magajin Shuwaram. Shi dai Shuwaram ya daɗe yana jagorancin ƙungiyar ISWAP wanda fitinannen mutum ne da ya addabi al'umma.
A ƙarƙashin ikon sa ne suk dinga tilasta wa jama'a a Ƙauyuka biyan kuɗaɗen haraji da da kuma biyan kuɗi domin yin noma wanda idan mutum bai biya ba za su hanashi zuwa gona kuma su lalata amfanin gonar. Haka kuma a ƙarƙashin shugabancin sa ne suka ringa kaiwa sansanin rundunar Sojin Najeriya hare-hare wanda yai sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin manyan jami'an.
Jama'a dai a jihar Borno na ta bayyana ra'ayin su kan nasarar da rundunar sojin ta yi na kai harin da yai sanadin mutuwar Sani Shuwaram da sauran mayaƙan kungiyar da dama wanda ba'a san iya adadin su ba wanda hakan ke nuna irin nasarorin da ake samu na yaƙi da ƴan bindigar.
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment