Amfanin zobo ga lafiyar ɗan adam - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Amfanin zobo ga lafiyar ɗan adam

Amfanin zobo ga lafiyar ɗan adam
Amfanin zobo ga lafiyar ɗan adam 


Zobo ganyen fulawa ne da muke jiqawa ko dafawa domin sha a matsayin lemo ko shayi domin jin dadi.


Da yawanmu da munsan amfanin zobo ga lafiyar mutum da mun qauracewa amfani da wasu da yawa daga cikin lemukan da suke yawo a kasuwa mun koma amfani da fulawar zobo.


Sanin muhimmancinsa yasa wasu kamfanunnuka yanzu suke sarrafa shi ya koma ganyen shayi ko kuma lemon gwangwaninsa.


Zobo na qunshe da sinadarai da suke taimakawa jiki ta fuska da dama, in ma ta hanyar tallafawa ko bada kariya daga kamuwa da ciwuka. Daga cikin amfanin fulawar zobo ga lafiyar dan adam sun hada da :-


-Tallafawa lafiyar kayan ciki ta hanyar samar da sinadaran da suke taimakawa wurin motsa kayan hanji yadda ya kamata.


-Qarfafa garkuwar jiki yadda idan ciwo ya kama mutum ba zaiyyi tasiri kamar a jikin sauran mutane ba.


-Fulawar zobo na taimakawa masu fama da hawan jini sosai ta hanyar relaxing jijiyoyin jiki yadda jini zai ringa zagayawa jiki ba tare da matsala ba.


-Ga masu fama da cinyewar gashi, fesa ruwan zobo a gashi na taimakawa wurin fito da gashi da kuma bashi sheqi mai kyau.


-Zobo na dauke da sinadaran Antioxidants da suke bawa jiki kariya daga kamuwa da ciwon daji (cancer).


-Shan zobo yana taimakawa wurin inganta lafiyar hanta yadda zata ci gaba da aikinta na tace abunda yake da illa ga lafiyar Dan adam.


Nr Sumayya Ibrahim Sa'ad 



Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel