Amfanin Yin Jima'i Ga Lafiyar Ma'aurata |
Duk abubuwan da kaga Allah (SWT) ya shirya ko ya kaddara to akwai hikima a ciki kuma sannan akwai amfanin sa. Allah shine ya halicci jinsi guda biyu wato na mace da kuma namiji domin hikimar sa sannan kuma ya tsara mu'amala a tsakanin su.
To wannan tsarin da Allah yai akwai hikimomi akai, akwai mu'amalar aure wacce itace ta haifar da wanzuwar dan adam a doron kasa. Wato hikima ko amfanin yin jima'i a samu mutane a doron kasa.
Sai kuma yaduwar al'umma ta hanyar jima'i wanda za muyi magana ne akan shi kansa jima'i da kuma amfanin Yin Jima'i ga dan adam.
Amfanin Yin Jima'i Ga Lafiyar Ma'aurata Tare Da Magance Cututtuka
Shi yin jima'i yana rage hawan jini ga masu yin sa. Duk yadda aka kai ga mace ko namiji suna yin hawan jini to idan suna yin jima'i za su rabu da wannan matsala ta hawan jini.
Sai kuma huce gajiya, a duk lokacin da jikin dan adam yai wasu ayyuka yasha wahala wanda zai jawo garkuwar jiki ya samu nakasu to idan yai jima'i zaiji kamar an sauke masa wannan gajiyar.
Amfanin Yin jima'i ko saduwa tsakanin mace da namiji na kara karfafa garkuwar jikin. Wato jikin zai samu karfi da lafiya, Shiyasa duk matar da aka yi jima'i da ita ya ratsa ta zakaga ranar ta zage tana yin aiki sosai.
Domin duk wanda yake yin mu'amala da mata yasan wannan. Sannan kuma yin jima'i yana gyara maniyyi domin fitar dashi yana kara samun lafiya ne da kuma inganta ruwan. Shiyasa idan mutum ba shida aure yake zama abin tausayi saboda baya fitar da maniyyi shi kuma idan baya fita yana dankarewa ne a mara.
Haka kuma yawan yin jima'i yana rage ciwo da cututtukan dake cikin jiki irin su ciwon kai ciwon jiki da ciwon gabobi. Duk mutumin da yake Jima'i ko dai mace ko namiji to zai rage masa wannan cutukan.
Sannan kuma yin jima'i yana rage ciwon zuciya. Idan mutum yana da ciwon zuciya to idan yana jima'i zai rage masa wannan ciwon ya samu sauki domin numfashin zai dinga fita cikin Kwanciyar hankali. Kuma mutum ba zai dinga samun bacin rai da bacin zuciya ba.
Sannan kuma yin jima'i yana rage wa mutum kiba da girman jiki. Irin abubuwa na abinci da mutum ke ci wanda suke kara kiba to idan yana yin jima'i za su ragu. Haka kuma yana gyara fatar mutum musamman mace zakaga fatar jikinta tana yin kyau tana sheki.
Ku lura da wannan idan mace ta yi aure daga baya za ku ga yanayin jikin ta ya sauya ta yi kyau ta yi haske musamman idan ta samu ciki za kuga ta canja. Yin jima'i kuma yana gyarawa mutum mafitsara indai ma'aurata suna yin jima'i za su samu gyaran mafitsara.
Shiyasa sau da dama idan ma'aurata sun yi jima'i zaka samu sunje sun yi fitsari. Shiyasa mazan da suke yin tafiya suna barin matan su ba tare da yin jima'i ba har tsawon watanni 5 ko shekara.
Ba duka mace ke iya jurewa ba suma mazan ba dukkan su ne ke iya daukar tsawon wannan lokacin ba tare da sun yi jima'i ba, saboda indai an saba yi to da wuya wani ko wata ta iya jurewa har tsawon wata ba su yi jima'i ba.