Amfanin Tsarki Da Ruwan Gishiri ga mace

Amfanin Tsarki Da Ruwan Gishiri ga mace
Ruwan Gishiri 


Mata sun kasance suna amfani da ruwan gishiri wajen wanke gabansu don magance cututtuka tun a zamanin baya, kuma bincike na likitocin wannan zamanin sun tabbatar da cewa hakan yana taimakawa.


Gishiri na da tasiri wajen kawar da cutukan bacteria da magance ƙaiƙayin gaba. Idan kuna fama da ƙaiƙayin gaba ku riƙa wanke gaban ku da ruwan gishiri, hakan zai taimaka muku magance dukkan wani ƙaiƙayin gaba da rage dukkan wasu cutukan dake a gaban mace.


Sai dai dolene a yi abin da kula, ba cikin farjin ake wankewa da ruwan gishiri ba, wajen farji (vulva) nan ake wankewa. Zaki fara wankewa da ruwa mai tsafta, sai ki sake wankewa da ruwan gishiri na minti daya zuwa biyu, ki dinga wankewa a hankali, sai ki sake wankewa da ruwa mai tsafta sannan ki goge gabanki da towel mara da datti.


Babban matsalar shine, da yawan gishirin da mata ke amfani dashi a kitchen yana da tarkace ko datti a cikinshi, tun daga wajen sayarda shi zuwa wajen ajiye shi, a sani dole a samu gishiri mai kyau.


Kuma ba a sanya ruwan gishiri kai tsaye a farji sai dai a ruwa, ba kuma cikawa ake yi ba, kadan ake amfani dashi.


Ba kullum ya kamata mace ta dinga tsarki da ruwan gishiri ba, sau 2 a sati ya wadatar.


Ba a zama a ruwan gishiri ko tsugunno, tsarki kawai ake yi dashi. Ku kasance tare da mu. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post