AMFANIN TAUNA ƘWAYAN KANANFARI — Android Pols
![]() |
AMFANIN TAUNA ƘWAYAN KANANFARI |
Ka samu kananfari ƙwaya biyu ka tauna ahankali (saboda yanada zafi) ka haɗiye,
1- Yana ƙara ƙarfin garkuwar jiki tahanyar yaƙan ƙwayoyin cututtuka dasuke ƙarya garkuwan jiki
2- Yana taimakawa wajen narkar da abinci musamman ga waɗan da suke da matsalar kumburin ciki ko taurin bahaya kamar basir, Ulcer ko tsutsar ciki. Anaso bayan ka haɗiye kasha zuma koda chokali ɗaya
3- Yana maganin tsatsan haƙori, ciwon haƙori ko haƙori mai kogo
4- Yana ƙara lafiyar hanta da kareta daga kamuwa da cuta
5- Yana rage raɗaɗi da zogi sannan yana rage kumburi ajiki
6- Yana warkar da ciwon gaɓoɓi da ciwon kai. Ana shafa Man kananfari awajen da yake ciwo.
7- Yana maganin infection
8- Yana sanya ƙamshin baki musamman idan a haɗashi da Na'ana ko girfa
9- Yana ƙara ƙarfin mazaƙuta da jimawa lokacin jima'i idan an haɗashi da namijin goro da Tomtom
Zaure Abu Muhaisin Islamic and Traditional Herbal.
Leave Comments
Post a Comment