Amfanin Man-zaitun ga lafiyar ɗan adam — Android Pols
![]() |
Amfanin Man-zaitun ga lafiyar ɗan adam |
Man-zaitun na da amfani sosai ga lafiyar 'dan adam, Binciken ilimin kimiyya ya nuna cewa man zaitun yana da amfani kamar haka:-
1. Yana 'karfafa garkuwar jiki ( domin yaki da kwayar cuta irin su bakteria, virus, fungus da sauran su.
- wadannan kwayoyin cuta ne masu haddasa matsalolin lafiya da dama, kamar irinsu typhoid, ciwon hanta , kurajen fata da sauransu.
2. Yana dauke da sinadarai masu bada kariya daga kamuwa da ciwon daji.
3. Yana dauke da sinadaran kariya daga cututtukan zuciya.
-yana rage yawan sinadarin kolesterol wanda idan yayi yawa a cikin jini yake da illa ga zuciya.
4. Yana dauke da sinadarai masu daidai ta hawan jini.
5. Yana taimako ga masu ciwon-suga.
6. Yana dauke da sinadarai masu rage ciwon jiki da ciwon gabobi kuma yana bada kariya daga ciwon jiki dana gabobi.
7. Yana inganta lafiyar zuciya, musamman ga tsofaffi wanda zuciyar su ta fara rauni wajen aiki saboda tsufa.
8. Yana bana kariya daga ciwon fata irin su daji dake shafar fata.
9. Yana dauke da sinadarai Wanda za su inganta lafiyar qashi.
10. Yana dauke da sinadarai Wanda za su inganta lafiyar kwakwalwa.
Allah ya qara mana lafiya
Leave Comments
Post a Comment