Amfanin Man-Zaitun Ga Dan Adam — Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Amfanin Man-Zaitun Ga Dan Adam — Android Pols

Amfanin Man-Zaitun Ga Dan Adam

Amfanin Man-Zaitun Ga Dan Adam 



Zaitun Da Man Zaitun 


Shi dai zaitun itaciyace mai albarka da kuma bada cikakkiyar lafiya a jikin dan Adam, kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja, kamar yadda muka samu bayaninta acikin ALKUR'ANI MAI GIRMA.


Haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan Manzon Allah (ﷺ)an karbo daga sayyadina umar yana cewa Manzon Allah (ﷺ) yace kuyi abinci da man zaitun kuma Ku shafashi ajikinku, domin hakika shi yana daga a cikin bishiya mai albarka. tirmizi ne ya ruwaito 


DAGA CIKIN AIKIN MAN-ZAITUN 


KARFIN MAZAKUTA, Duk mutumin da ya samu kanshi a wannan hali, to ya samu garin habbatussauda ya dinga zubawa acikin ruwan danyan kwai sannan a Soya shi da man zaitun ya dinga ci. Kullum , insha Allah zai samu karfin mazakuta sosai. 


Kada ka gaji duk wani magani da kagani ka gwada zaka dace insha Allah 


CIWON CIKI; Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatussauda ya cakuda ya sha safe da yamma. Ya samu kamar sati daya yana sha ko kina sha insha Allah_


CIWON KAI; Duk mutumin da yake ciwon Kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali daya da safe da Rana da dare insha Allah zai samu lafiya. 


CIWON HAKORI; duk mutumin da yake ciwon hakori sai ya samo ganya zaitun da ya'yan habbatussauda ya sakasu acikin garwashi ya buda bakinsa hayakin ya dinga shiga, insha Allah._


CIWON HANTA; duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan manzaitun cikin cokali daya da safe daya da Rana daya da dare. 


CIWON DADASHI; Duk mutumin da yake ciwon dasashi sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa da shi. 


CIWON SUKARI; duk mutumin da ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana hadawa yana sha kafin ya kwanta bacci insha Allah. 


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel