Amfanin kanunfari 7 ga lafiyar Dan Adam — Android Pols
![]() |
Amfanin kanunfari 7 ga lafiyar Dan Adam |
Mafi yawan Mutane Suna Kallan Kaninfarine kawai domin Sanyawa a shayi ko kayan kamshi irin na yaji da makamantansu.
Amfanin kaninfari bai takaita iya nan kawai ba, domin yana maganin abubuwa da dama kamar:
1 ) CIWON HAKORI: dandaqashi akeyi a lika cikin hakorin.
2 ) BASUR: jikashi ake ya tsumu, kullum sai asha cokali uku da safe da dare.
3 ) MAGANCE MATSALAR WARIN BAKI: jikashi ake da lemon tsami da garin habbatsusauda a dinga kuskure baki dashi kullum da safe da rana da dare.
4 ) WANKE JINI: jikashi ake da tsamiya a dinga sha sau daya Kullum.
5 ) MAGANAR LARURAR SIKILA:Tafasashi akeyi tare da Zogale a dinga shan ruwan ana cinye ganyen.
6) KORAR MACIZAI DAGA GURI: Yadda mata Suke turaran kamshi, idan aka Dan zuba ko guda bakwai ne a cikin garwashin, to macizai basu zama a gurin, idan akwai suma sai sunyi kaura sun bar wajan.
7 ) MAGANCE MATSALAR WAHALAR HAIHUWA: Kullum me ciki ta dinga Samun kaninfari tana taunawa kamar gudu uku tana hadiye ruwan yawun bakinta idan ta tauna. Da yardar Allah ba zatayi doguwar nakudaba ko kuma ace ta wahala wajan haihuwa.
Ya Allah ka cigaba da wadatamu da lafiyar Zuciya da gangar jiki gaba daya.
A yi sharing din wannan post din don sauran yan uwa ba su gani su karu suma.
Allah yasa adace
Leave Comments
Post a Comment