Amfanin Ganyen Magarya Da Garin Magarya Ga Lafiyar Dan Adam
![]() |
Amfanin Ganyen Magarya Da Garin Magarya Ga Lafiyar Dan Adam |
Bismillahi Rahmanir Rahim.
Itaciyar magarya wadda akafi sani da (Assidir) a larabce kuma (Lote) a turance, itaciya ce mai albarkatun da dadewa Annabi S.A.W ya tabbatar da amfaninsa.
Magarya yana kunshe da magunguna masu matukar mahimmanci ga jikin dan Adam kuma yana da karfin kashe kwayoyin cuta cikin dan kankanin lokaci.
Magarya Antibiotic ne mai karfin gaske kuma cikin ikon Allah bashi da wani illa wato side effects na azo agani.
Amfanin Ganyen Magarya Da Garin Magarya Ga Lafiyar Dan Adam
Amfanin magarya suna da yawa sosai, bazan iya kawo muku su duka ba, amma ga kadan daga cikin wasu amfanin kamar haka ;
1.Ciwon daji (cancer) : Idan ana dafa garin magarya ana sha da zuma yana kashe kwayar cutar daji koda a cikin jini ne idan kuma Yayi miki sai a rinka dafa garin magaryar da ruwan khal ana wanke wurin mikin idan an wanke sai a barbada garin magaryar.
2. Yana da karfin yakar cutar fata kamar su tautau, maker, Karzuwa da sauransu. Ana kwaba shi da zuma a rinka sha Ana shafawa a Wurin da abin ya shafa.
3. Yana tsaftace jini domin Yana dauke da sinadarin Saponin,alkaloid da triterpenoid wadannan Sinadarai ne masu tsaftace Jini.
4. Shansa da ruwan zafi yana magance gajiya da ciwon Jiki.
5. Yana magance ulcer idan ana shansa da madara ko zuma.
6. Yana taimakawa hanta ya hana shi jin ciwo da cututtuka.
7. Yana daidaita nauyin mutun.
8. Yana tsaida zawo cikin kankanin lokaci idan aka Shashi da ruwa ko koko.
9. Yana mikar da kasusuwa musamman ga mai karaya.
10. Yana maganin rashin shaawa ga mata idan suna tsarki dashi kuma Suna shansa da madara.
11. Kuma a karshe dai yana warware sihiri a cewar malaman sunna Idan aka jika garin a ruwa tare da karanta wasu ayoyi daga cikin Alqur’ani mai girma.
Allah yasa mu dace.
Leave Comments
Post a Comment