Amfanin daddawa ga lafiyar ɗan adam — Android Pols

Amfanin daddawa ga lafiyar ɗan adam
Amfanin daddawa ga lafiyar ɗan adam


Daddawa na daga cikin abincin mu na gargajiya da muke amfani da ita yau da kullum wurin girki domin qarin dandano da qanshin abinchi.


Amma amfanin daddawa ba Iya nan ya tsaya ba domin kuwa :-


-Daddawa na daga cikin abincin da yake taimakawa masu hawan jini da ciwon siga.


- Akwai sinadarin qara qarfin ido a ciki.


-Daddawa na qunshe da sinadarin fiber da suke taimakawa wurin fitar da bayan gida ba tare da ansha wahala ba.


-Akwai sinadaran da suke taimakawa wurin samun daidaiton kitsen jikin mutum wanda hakan zai sa a samu jijiyoyi masu lafiya da ingancin lafiyar zuciya.


-Akwai sinadaran da suke taimakawa wurin samun garkuwar jiki (Immunity) a cikin daddawa.


-Sinadarin Calcium ya shahara wurin taimakawa lafiyar qashi ga qwarinsa, to shima akwai shi a daddawa.


Amfani da daddawa abune mai kyau amma don Allah Idan za'ayi girki a dafata ta  dahu domin a rage qarfin ta Idan danya ce kenan.


Yanada kyau bayan anchi a ringa wanke baki ko asuwaki kafin shiga cikin jama'ah domin ba kowa ke son qanshin ta ba.


Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad 

RN,RM,PND 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post