Amfanin cucumber ga lafiyar ɗan adam — Android Pols
![]() |
Amfanin cucumber ga lafiyar ɗan adam |
Cucumber na daya daga cikin kayan lambu da yake da sauqin samu a kasuwannin mu na birni da karkara.
Ana amfani dashi a matsayin mahadi na kayan salad, ko kuma a yanka shi shi kadai a ci da abinchi, wasu lokutan kuma ana yin kwadonsa aci haka.
Masana sirrin hada lemo ma basu barshi haka ba domin ana sarrafashi ya koma abun sha ko a hadashi da wani abun sha kamar zobo domin qarin dandano da saka qamshi.
Ko ma dai ta hanyar aka zabi amfani dashi hakan yana da kyau ga lafiyar mutum. Saboda amfanin sa ga lafiyar mutum wasu kamfanunnuka yanzu suke sarrafa shi ya koma lemo ko sabulu, man shafawa ko kuma turaren fesawa a jiki saboda muhimmancinsa ga fata da sauran jiki.
Daga cikin amfanin cucumber ga lafiyar mutum sun hada da :-
-Hydration Sama da kaso casa'in (90) na cucumber ruwa ne, wanda hakan damace musamman a wannan yanayin na sanyi da muke ciki da ba'a fiye shan ruwa ba, amfani dashi zai taimakawa jiki wurin samar da ruwan da jiki zaiyyi aiki dashi koda mutum baisha ruwa da yawa ba.
-Amfani da cucumber a fata yana taimakawa wurin cire sun burn, kumburin ido (puffy eyes) da hana yamushewar fata.
-Cucumber yana dauke da vitamin da mineral kamar su Vitamin B1,B2,B5,B6,B9, Vitamin C&K, Cu, Zinc,Mg,Mn, K,P da sauran su duka wadannan sinadarai ne da jiki yake buqata wanda idan aka dauki duk duk daya a cikin su shima yanada da nasa bayanin da irin muhimmancinsa ga jiki.
-Yana dauke da sinadaran da suke bawa jiki kariya daga kamuwa da ciwon daji (cancer).
-Harkar gashi ma ba'a barta a baya ba domin cucumber na dauke da sinadaran taimakawa wurin fito da gashi.
-Ga masu yawan gyatsa da cushewar ciki amfani da cucumber zai taimaka wurin rage hakan sosai.
-Cucumber yana taimakawa hanji ta hanyar samar da motsinsa yadda ya kamata.
-Cucumber yana taimakawa jiki wurin fitar da abunda yake da illa a cikinsa.
-Ga masu son dai-daita nauyin jikin su ko rage qiba da tumbi, Cucumber ya kamata ya zama daya daga cikin kayan abincin ku na yau da kullum.
-Masu fama da matsaloli irin na fata kamar large pore, dark circle, cellulite amfani da cucumber na cikin hanya mafi sauqi na magancesu ba tare da an illata fata ko kashe kudi ba.
Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad
RN,RM,PND
Leave Comments
Post a Comment