Amfanin Ayaba ga rayuwar dan Adam — Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Amfanin Ayaba ga rayuwar dan Adam — Android Pols

Amfanin Ayaba ga rayuwar dan Adam

Amfanin Ayaba ga rayuwar dan Adam 



Ayaba na daya daga cikin kayan marmari masu dandano da qamshi mai dadi musamman idan an samu mai kyau.


Akan yi amfani da ita wurin sarrafa kayan qwalam da maqwalashe ko kuma aci haka.


Tana qunshe da sinadarai masu fa'ida sosai da suke taimakawa jiki wurin bayar da kariya, qarin lafiya da kuzari da sauran su.


Amfanin Ayaba ga rayuwar dan Adam 

 

Daga cikin amfanin Ayaba a jikin dan adam akwai :- 


-Taimakawa masu juna biyu da suke fama da laulayi musamman a watannin farko.


-Samar da sinadarin Calcium wanda yake qarawa qashi qwari da lafiya.


-Samar da kuzarin jiki 


-Tallafawa lafiyar hanji ta hanyar motsashi yadda ya kamata.


-Hana taruwar bayan gida a ciki.


-Inganta lafiyar zuciya da qwaqwalwa.


-Bayar da kariya daga kamuwa da ciwon daji.


-Taimakawa masu fama da gyambon ciki.


-Gyara fata da gashi.


-Taimakawa masu son dai-daita nauyin jikin su ko rage qiba 


-Taimakawa wurin rage zafin ciwon mara lokacin jinin Al'ada.


-Samar da nishadi da rage ciwon damuwa.


-Taimakawa jiki wurin samar da qwayoyin halittar jini da hana qaranchin jini a jiki.


-Hana qwannafi da tashin zuciya ga masu ciki.


-Da sauran su.


Nr Sumayya Ibrahim Sa'ad 


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel