ƘALUBALEN DA MATAN DA AKAYI WA YANKAN GISHIRI SUKE Fuskanta - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

ƘALUBALEN DA MATAN DA AKAYI WA YANKAN GISHIRI SUKE Fuskanta

ƘALUBALEN DA MATAN DA AKAYI WA YANKAN GISHIRI SUKE FUSKANTA

ƘALUBALEN DA MATAN DA AKAYI WA YANKAN GISHIRI SUKE FUSKANTA


-Kasancewar ba'a allurar kashe zafi ko shan maganin kashe ciwo kafin ko kuma bayan yankan gishiri dole za'a ji ciwo fiye da tunani domin sai an girma sosai akeyi.


-Hadarin kamuwa da qwayoyin cututtuka 

Yankan gishiri na daya daga cikin hanya mafi sauqi ta daukar qwayoyin cuta saboda kayan da ake amfani dasu na kaifi ba masu tsafta bane,kuma ba'a kashe qwayoyin cututtuka dake jiki ba (not sterile).Amfani da qarfe irin wannan zai iya haifarwa da mace kamuwa da Pelvic Inflammatory Disease, Ciwon sarqe haqora(Tetanus), Urinary Tract infections da sauran ciwuka wanda zasu iya hana mace daukar ciki da sauran ciwuka.


-Ana samun zubar jini mai yawa saboda rashin ilmin abunda ya shafi jikin mutum (Anatomy)zai iya sakawa a taba wata jijiyar da jini zai ta zuba, wanda hakan ba qaramar matsala bace.


-Akwai wadanda ko da anyi musu yankan gishiri suna iya daukar ciki, amma kuma suna gamuwa da larurori lokacin da suka zo haihuwa wadanda sun hada dasu doguwar naquda (Prolonged labor) ko qaruwa fiye da tunani saboda an yanke bangaren da zai iya budewa (stretch) lokacin haihuwa ba tare da matsala ba saboda akwai elastic tissue wurin.


-Sakamakon cire naman wurin da akayi, tunda ba zuwa asibiti za'ayi a duba a dinke wurin da yake buqatar dinki ba, dole Idan wurin ya tashi warkewa ba zaiyyi yadda ake so ba, domin inda ba'a  so ya hade zai hade. Dalilin  haka dole za'a ringa jin zafi da discomfort lokacin yin fitsari da jinin al-ada.


-Idan wani abu mara dadi ya faru da mutum musamman idan an mallaki hankali,zaiyyi wahala a manta domin lokaci zuwa lokaci mutum zai ringa firgita Idan ya tuna wanda akan kirawo shi da Post Traumatic Stress Disorder (PTSD), ba iya wannan bama dole rayuwar duk wanda akayiwa yankan gishiri ta canja tun daga yadda mutum zai ringa kallon kansa (body image and self-esteem).


-Fuskantar matsaloli da miji lokacin  mu'amalar aure.


Halittar Clitoris a jikin mace shine sensitive organ, cireshi kan haifar da tsananin jin zafi da rashin jin dadi ga mace wanda hakan na haifar da matsaloli a gidajen aure da kuma rayuwar mace gaba daya.


Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad 

RN,RM,PND


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel