Allah Gwani | Ko Ka San Menene Ayyukan Hanta A Jikinka?
![]() |
Ayyukan Hanta A Jikinka |
Nasan da yawa daga cikin mutane basu san menene ayyukan da hanta ke yi jikin dan adam ba. Hakan yasa yau na kawo muku wasu daga cikin muhimman ayyukan da hanta ke yi a jiki kamar haka;
1. Hanta guda ce daga cikin muhimman kayan ciki. Kuma tana nan a cikin ciki a ɓangaren dama daga sama, ƙasa da faffaɗar tsokar nan da ta shingice tsakanin ciki da ƙirji.
2. Nauyin hantar mutum ya kai nauyin kilogiram É—aya da rabi (1.5kg).
3. Hanta na samun jini da ya kai yawan lita É—aya da rabi (1.5L) a kowane minti É—aya.
4. A hanta ne ake gama narka sinadaran abinci yadda jiki zai iya amfani da su kamar dangogin siga, furotin, kitse/mai, magunguna, bitamin da sauransu.
5. Hanta taska ce da ke ajiye muhimman sinadarai zuwa lokacin da jiki zai buƙace su, kamar siga, narkakken furotin, nau'o'in bitamin da sauransu.
6. Hanta na samar da sinadarai kamar gulokos, narkakken furotin da sauran muhimman sinadaran da jiki ke buƙata.
7. Hanta ce ke samar da ruwan maɗaciya. Ruwan maɗaciya na amfani wajen narka abinci ajin kitse/mai yadda jiki zai iya zuƙar kitse/mai daga ƙaramin hanji zuwa cikin jini sannan jini ya kai shi zuwa dukan sassan jiki.
8. Hanta na yin aikin kawar da guba, muggan sinadarai da ƙwayoyin cuta kamar bakteriya da bairos.
9. Hanta na sarrafa / samar da jini ga É—an-tayi, haka nan, tana ajiyewa da samar da muhimman kayayyakin sarrafa jini kamar sinadaran 'vitamin B12' da 'Iron'.
10. Jajayen ƙwayoyin jini na shafe kwanaki 120 suna rayuwa ne a jiki. Bayan saifa, hanta na daga cikin sashin jiki da ke kashe raunanan jajayen ƙwayoyin jini bayan sun cika kwanaki 120 suna aiki.
11. Hanta ce sashin da ke samar da mafi yawan zafi/É—umi da jiki ke amfani da shi wajen ci gaban rayuwa.
12. Hanta ɓangare ne na garkuwar jiki. Domin hanta na samar da sinadaran da ke yi wa garkuwar jiki ƙaimi, bayan nan, tana yaƙar baƙin abubuwa da ke shiga jiki ta hanyar abinci, harbin ƙwayoyin cutuka da sauransu.
Wannan sune wasu daga cikin ayyukan da hanta ke yi a jikin É—an adam. Da fatan kun ilimantu.
©Physiotherapy Hausa
Leave Comments
Post a Comment