Alamomin da kawaye zasu lura dasu don gane ƙawa yar lesbian — Android Pols
Alamomin da kawaye zasu lura dasu don gane ƙawa yar lesbian |
Kafin mu tsinddima cikin wannan tattaunawa, yana da kyau mu sani cewa, kamar yadda maza suke farautar mata don suyi lalata dasu, haka yanzu mata suke farautar mata yan uwansu don su yi lalata su. Daga cikin su akwai masu yi sannan akwai dillalai da masu recruiting kananan mata. Kuma suna amfani da kudi, ko kawaye, ko wuraren sana'oi don cinma wannan manufa. Kuma kowa zai iya zama target. Don haka a lura sosai.
Allah ta'alah yana fada a cikin Qur’ani cewa kar mu yi zargi, sannan kada muyi zato, sannan kada mu yi kage. Don haka mu lura da kyau, lalle ne ace wanda yake da wannan alamomi yana yi ba. A bari hujjojin su bayyana karara kafin a yanke hukuncin. Sannan yana da kyau mai karatu ya sani, wannan rubutu Research aka yi sosai kafin gabatar da shi. Sannan wasu masu alamomin nan ba lalle ace suna yi bane.
Target location:
Wurare da ake zuwa don recruiting mata sun hada da wajen sana'oi irinsu wajen kitso, wajen kwalliya, wajen koyan sana'oin mata. Sannan ana amfani da masu Event centres da masu hotuna. Mai hoto zai iya approaching din ki a wajen dinner ko taro ya miki hoto kyauta sannan ya karbi number ki. Bayan biki zai turawa mata da maza kawalai, idan kin musu zai kira ki da niyyar kizo ki karbi hoton, wani ma har ya baki kudi ya ce wai an ganki ana son ki. Daga nan idan baki da wayo shikenan sai dai wata ba ke ba. Sannan akwai joints na cin abinci da shakatawa. Manyan mata suna zuwa don farautar kananan mata. Su kashe miki kudi su karbi number. Shikenan sai ki jira appointment. Kuma yana da kyau ki sani cewa majority nasu matsafa suke wa aiki. Tsafin kudin suke. Don haka ki san me kike shiga.
Alamomin kawa yar lesbian sune kamar haka:
1. Romantic messages. Kawa zata rika turawa kawa sakonni masu kama da irin wanda namiji da mace ne kadai suke exchanging. Sakonni masu narka zuciya.
2. Romantic compliments. Mace ta rika yaba kyan mace yar uwarta har yabon yayi yawa. Misali you are sexy kawata. Duk Namijin da ya same ki ya more. Irin wannan diri haka. Kai gaskiya ina son irin jikinki. Da sauransu.
3. Crushing women. Mace ta rika son mace yar uwarta har tana ma fada cewa gaskiya ina son wacce.
4. Texting and calling obsessively. Mace ta rika kira da texting mace ba dare ba rana, sai kace sabon saurayi da budurwa.
5. Sharing her intimate moments. Mace ta rika gayawa mace zancen sexuality dinta ko kuma batsa don ta tayar wa da yar uwarta mace sha'awa. Ko ta rika bata labarin yadda take so namiji yayi da ita akan gado.
6. Sharing pijamas. Mace ta rika tura miki hotunan kayan baccin ta don ki gani.
7. Twinning wato Anko. Mace ta rika son kuyi anko akan komai don ta gina soyayyar ta a zuciyar ki. Kuma anan ba maganar ankon biki ake ba.
8. Status updates. Mace ta rika saka hotuna a status, hotunan da bai dace wani ya gani ba. Sai tayi setting exclusion na contact list dinta don ke kadai ki rika gani. To ta rika saka ki a status don ki ji kamar ke ta musamman ce a wajenta.
9. Bana sha'awar maza. Sannan duk sanda akai maganar maza a cikin kawaye sai ta rika cewa ita bata son maza ko sha'awar su bata yi.
10. Telling you she loves you. Ta rika gaya miki tana son ki. Ta rika cewa Fatima ina jin ki a zuciyata, ina son ki. Ina kaunar ki. Ta fada a message, ta fada a waya. Ko ina.
11. Quickly breaking up with friends. Idan tayi tayi kika ki bata hadin kai. Yanzu zata daina kula ki. Hakakawai sai kiga mace kun yi breakup baki mata komai ba.
12. Always jealous and quiet when you talk about your boyfriend. Duk sanda kika zo da zancen saurayin ki sai ta rika bata rai. Bata so. Kuma wata har sai ta nemi ta raba ku.
13. Always want to be alone with you. Duk yadda za tayi sai tayi don ku rika kebewa ko mu'amala a cikin duhu. Har ma ta rika kai miki hannu kamar mistake ne amma gwada ki take.
14. Taking you out on a date. Da ta samu kudi sai ta gayyace ki kuje cin abinci ko shan ice cream ko cin shawarma. Kamar yadda namiji zai.
15. Always needing your attention. Tana so ki rika bata attention. Har idan ma baki bata ba zata rika fishi har da kuka. Idan kina da aure ma har bata so ace mijinki ya dawo. Sannan haka kawai sai kiga ta raina mijin ki. Wai jininsu bai hadu ba. Karya take.
16. Always stripping naked in front of you. Idan kuna tare bata kunyar ta bayyana tsiraici a gabanki. Kuma bata ki ta kai miki hannu ba idan taga kin tube. Sannna tana so tace ku yi wanka tare.
17. Son jiki. Idan kuna tare niki niki ta kwance jikin ki. Tayi ta shinshinaki tana shasshafa ki kamar bata san me take ba. Idan kika kamata sai tace wasa ne.
18. Yabon ki a gurin mutane kuma ba wani abu kika mata na yabawa ba. Amma duk inda akai zancen ki itace lawyer din ki.
19. Yi miki introducing porn don ku fara kebewa kuma tana saka ki sha'awa.
20. Sleep over. Tana so ta rika zuwa kuma kwana tare. Idan mijin ki yayi tafiya tana so tazo.
21. Daga haduwa da wata kawa a saloon, ko gidan lalle ko gidan makeup kawai sai tace tana son ki don Allah har kuyi exchanging numbers. Next time zata zo gidan ku. Daga haduwar gidan kitso har ta kulla alaka.
22. Idan yar tiktok ce ko snap, to zata rika hawa wakokin soyayya, daidai baitin da namiji yake wa mace, sai kaji tana yi azuwan ita namiji ce. Misali, sai mace ta hau wakar Hamisu Breaker wadda shi Hamisu mace yake bege. Itama sai ta hau wannan waka tana begen wata mace yar uwarta. Misali kamar yadda wasu yan wasan Hausa su biyu suke wa junansu. Idan yau wannan tayi anjima sai dayar tayi.
23. Kawai mace ta ganki a super market ta biya kudin shopping kuma ta baki number.
Part 3. Alamomin da Miji zai lura idan matarsa na yin lesbian.
To be continued...
----
Muhammad Ubale Kiru
Leave Comments
Post a Comment