Abubuwan Dake Jawo Rashin Kuzari Ga Magidanta A Yayin Kusantar Iyali —Android Pols

Abubuwan Dake Jawo Rashin Kuzari Ga Magidanta A Yayin Kusantar Iyali
 Rashin Kuzari Ga Magidanta A Yayin Kusantar Iyali


Duk abubuwan da muke bayarwa wanda ya shafi lafiyar jikin mata da maza mu kan yi bayani iya daidai gwargwadon fahimtar mu. Wanda a yau insha Allah za mu yi bayani ne akan abinda ya shafi karfin maza da abubuwan da ke sa su rashin karfin ko kuma idan ana cikin saduwa sai gaban ya kwanta.


Mutum yana cikin saduwa da iyalinsa ga gaban nasa ya mike amma da zarar ya fara saduwa sai gaban nasa ya kwanta kamar wani lagwani shikenan kuma ba zai kara mikewa ba sai wani lokacin. 


To menene dalilin faruwar hakan? Menene yake jawo rashin karfin gaba da kuma kwantawar sa? Akwai dalillai da yawa da suke jawo hakan shiyasa a yau muka kawo muku wasu daga cikin su kamar haka;


(1) Basir, Zafi Ko Dan Kanoma:

wannan matsala ce da kan takurawa maza, musamman wani yakan yi tsiro yakan je wajen uwar hanji ko dubura yaje ya zauna. Jijiyoyin da suke dubura da maraina da gaban mutum suna tafiya ne baki daya wanda hakan ke haifar da mutuwar gaban mutum. Wanda hakan ke jawo gaban mutum ya mutu gabaki daya har kaji ana cewa anyi masa asiri, to ba asiri bane matsala ce ta basir.


(2) Ciwon Suga:

Duk mutumin da yake da matsalar ciwon suga zai iya samun wannan matsala ta rashin kuzari domin ruwan jikin sa da jinin jikin sa suna aiki wanda a dalilin wannan ciwo na suga yakan hana kaiwa da komowa na jini a jikin mutum. Shi kuma gaban mutum jijiyoyi ne wanda sai jiki ya motsa shima yake motsawa.


(3) Hawan Jini:

Hawan Jini shima yana da tasiri ga mazakutar dan adam, idan mutum yana da hawan jini wanda yai karfi a jikinsa to shima zuciyar ka ba za ta buga yadda ya kamata ba sai gaban ya dinga kwantawa.


(4) Sanyin Mara:

Yadda mutum zai gane yana dauke da sanyin mara shine sha'awar sa ma daukewa take yi gabaki daya. Mutum zaiji ba ya jin sha'awa gabaki daya, sannan kuma idan kazo saduwa da iyalin ka sai gaban ya kwanta. kana kawowa sai gaban ya kwanta kamar ba'a yi wani abu ba.


(5) Shekaru:

Idan mutum shekarunsa suka ja to ba zaiyu yace zai ji karfi da sha'awa ba kamar yadda ya saba yi a baya ba hakan ba zai taba yuwa ba. Idan shekarun mutum sun kai 60 zuwa sama to dole ne yaji rauni a tare dashi ba kamar lokacin yana da shekaru 30 ba.


Wannan sune abubuwa 5 ko matsaloli dake haddasa rashin karfin gaba da kuma rashin sha'awa da rashin kuzari ga namiji . To duk wanda yaji yana fuskantar irin wadannan matsaloli to sai yai gaggawar neman magani domin samun mafita.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post