Abubuwan Da Ya Dace ku Sani Kan Makabartar Al-Shabeka Dake Masjid al-Haram — Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Abubuwan Da Ya Dace ku Sani Kan Makabartar Al-Shabeka Dake Masjid al-Haram — Android Pols

Abubuwan Da Ya Dace ku Sani Kan Makabartar Al-Shabeka — Android Pols
Abubuwan Da Ya Dace ku Sani Kan Makabartar Al-Shabeka Dake Masjid al-Haram


Makabartar Al-Shabeka tana kudu maso yammacin Masjid al-Haram. Kafin zuwan Musulunci wasu daga cikin maguzawan larabawa sun kasance suna yin aikin jahiliyyah na binne 'ya'yansu mata da rai, su na ganin haihuwar ya' mace abin kunya ne. An ce anan ne ake binne su a makabartar Al-Shabeka. Haka kuma an ruwaito cewa an binne Sumayyah (رضي الله عنها). Sumayyah ita ce mutum ta farko da ta farayin shahada a tafarkin Musulunci.


Al'adar kashe mata a al'ummar Makkan jahiliyya


Daya daga cikin munanan ayyukan al'ummar jahiliyya shi ne binne 'ya'yan fari da rai idan mace ce. Manyan mutane ba sayin haka. Wannan ya na faru ne a cikin gama garin talakawa. 


Idan haihuwar farinsu mace ce, sai su binne ta da rai don hadaya ga gumakansu. Allah (ﷻ) ya mayar musu da martani a cikin Alqur’ani ga wadannan iyaye yadda suke ji a lokacin da aka haifa musu ‘ya mace:


Duk lokacin da aka yi wa ɗayansu albishir da haihuwar ya' mace, sai fuskarsa yi baƙikkirin, sai su danne fushinsu. Su boye kansu ga mutane saboda munanan labarin da su ka samu. Shi ya kunyata, ko kuwa ya binne ta a cikin ƙasa da rai? Haƙĩƙa, tir da hukuncinsu. Suratul Nahl 16:58-59.


A ranar kiyama za a tambayi yarinyar da ba ta da laifi, dalilin kashe ta. Za ta ba da labarin irin zaluncin da baragurbin iyayenta  suka yi mata na binne ta da rai:


Kuma za a tambayi yarinyar (wacce aka binne) da ranta da wane laifi aka kashe ta?. Suratul Takwir 81:8-9.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel