Abubuwan Da Ya Dace ku Sani Kan Larurar Gaggautowar Saurin Balaga [Precocious Puberty]

Abubuwan Da Ya Dace ku Sani Kan Larurar Gaggautowar Saurin Balaga [Precocious Puberty]
Saurin Balaga 


Menene Saurin Balaga? Balaga da wuri wanda a turance ake kira da (Precocious Puberty) Wani yanayi ne na tangarɗar halitta dake haddasa gaggawar bayyanar balaga tsakanin kananun yara Mata kafin su cika shekara 8 a duniya, da kuma ƙananun yara Maza tun kafin su kai shekaru 9 da haihuwa. 


Toh sai dai anfi gani da saurin shaida matsalar nan da nan a yara Mata duba da halittunsu sune suke kusan bayyane ƙarara (nono) saɓanin rukunin Maza.


Waďannan suffofin balagar da ake gani a yara Mata su ne kamar haka; 

  • Bayyanar girman nonuwa a kirji
  • Bayyanar kurajen pimples
  • Bayyanar gashin hammata
  • Bayyanar gashin Gaba, da kuma
  • Fara jinin haila


Duk ana ganinsu ne tun kafin yarinya ta cika shekara 8 a duniya kamar yadda bincike ya bayyana.


Yayin da a ɓangaren yara Maza alamun da iyaye kan fara gani na fara balagar su sune:


  • Girman jakar ƴaƴan maraina yaro (scrotum)
  • Gashin gaba cunkus (Pubic hair)
  • Girman azzakari kamar na babba
  • Gashin hammata da na fuska (gemu) 
  • Karyewar murya zuwa ta manya 


Duk wadannan na faruwa ne ga yaro tun kafin ya cika shekaru 6 a duniya.


Menene Ke Haddasa Saurin Balaga Ga matasa? 


Hakan na faruwa ne a sakamakon tangardar aikin wata halitta a kwakwalwa da ake kira da (pituitary glands) wanda shi ke ƙunshe da rassa "6" kimanin shida. 


Wanda rassan shida kowannensu da abunda yake samarwa, Kama daga samar da sinadaran dake taimakawa wajen jima'i, narkar da abinci, tace jini, girman jiki, ƙwarin ƙashi, daukar ciki, girman nonuwa, tsatstsafowar ruwan nono, fitsari, naƙuda, jinin haila, samuwar maniyyi da sauransu. 


Toh guda 1 cikin rassa 6 dinne na fituitary sai reshen dake samar da sinadaran haihuwa, sha'awa, jima'i, maniyyi, wankin mahaifa da jinin haila ke samun matsalar dake sashi fara sakin duk wadancan sinadarai na (istrojin, furojesteron, ds) wanda za su bayyanar da wadancan alamomin cikar halittar Mace ko Namiji tun kafin lokacin da ya dace su fara bayyana wato tsakanin shekaru 12 zuwa 16 na rayuwa.


Wannan shine gaggawar balaga, wanda ya bambanta da saurin balaga da ta saba zuwa lokacin da ake tsammani.


Shi Kuma Saurin Balaga [Early Puberty]


Kamar yadda nace a hannu guda kuma baya ga FIRIKOSHUYOS Akwai kuma wata makamanciyar matsalar da akewa laƙabi da Early puberty wato saurin balaga. Shi kuma precocious kamar gaggautowar balaga.


Anan shi saurin balaga (Early puberty) shi ma duk ana ganin wadancan suffofin na bayyanar nonuwa tsir-tsir a kirjin yarinya, kuma ƙila idan ta matsa kan taga hadda ruwa, fara haila, canzawar warin jiki, pimples da bayyanar gashin jiki ga Mace. 


Haka ma girman ƴayan maraina, karyewar murya, fitar maniyyi, girman azzakari da duhun matse-matsi, gami da canzawar warin jiki ga yaro Namiji.


Sai dai anan za'a samu Yarinyar ta baiwa shekaru 8 baya, wato tana tsakanin shekaru 9 zuwa 11, yayin da shi kuma namijin zai zamto bayan ya baiwa shekaru 9 baya amma bai kai 14 ba. In kun lura kenan shekaru ne suka bambanta amma duk alamun daya ne.


Shi ma wannan waccan matsalar ta tangardar halittar da nace itace de kan taka rawa wajen faruwarta anan ma. 


Toh sai dai anan sauran abubuwa da dama da akan alaƙanta faruwar hakan dasu sune: 


- Hutun rayuwa da samarwa yaro abunda duk ya nema ko bai nema ba na ci ko sha, ba tare da ana saka shi yana motsa jiki ba


- Ciye-ciyen abinci marasa kyawu ga jiki wato junks foods; irinsu pizza, Samosa, burger, dognut da sauran abubuwan zaƙi da maiƙo, ba tare da ana komi na motsa jiki yadda za'a konasu ba, da kuma yaran da ake yawan basu abincin waken suya suna ciki kullum-kullum saboda tasirin pyoestrogen dake kunshe ciki.


- Da kuma samuwar sabbin hanyoyin girki da dumama abinci na zamani irinsu: Ovun, Teflone cookwares, nonstick wrappers, chemicals da ake amfani dasu wajen gine-ginen zamani da fenti, rashin kwanciya bacci da wuri ga yaro abarshi yai ta kalle-kallen tv ko video game, da dai sauran abubuwa wanda mukan iya ci, shaƙa ta iska ko sawa a fatar jikinsu cikin kayayyakin kwalliyar da ake shafawa yara,


- Da kuma karikitai da iyaye Mata suka duƙufa amfani dasu da sunan karin ni'ima a jika da sassake-sassake na herbal concussion wanda Mata basa fasawa koda suna dauke da juna biyu. wanda wani abun na rashin kan gado sai ciki ya samu ma ake farwa. wanda yawanci wannan abubuwan suna da abunda ake kira TERATOGENIC EFFCTS domin suna iya kutsawa shiga Mahaifarki inda jariri ke kwance su barshi da illah. 


Shiyasa zakuga ko Maganin asibiti in Mace na da ciki bakowanne aka yadda tasha ba. 


Shiyasa ko yaushe nakance mutane su san abu kafin kasa shi jikinka ko cikinka, ba wai kurum don kaga kowa nayi ba. Wani zaiji asama na ambaci hadda madarar waken suya ko irinsu awara yai mamaki. Eh kya iya kita bawa yarki kuma Allah yasa hakan bai faru ba wannan kuma ya danganta da yadda jikin kowa ke maida martanin abu, domin akwai wanda jikinsa ko ya yaji bakon abu zai canza. 


Babban misali allurar Kulorokuin ai ba kowa take sawa kaikayi a jiki yai ta susa ba, wani ko nawa akai masa lafiya zai zauna, wani ko babu lafiya in akai masa. Haka wani zai iya cin gyada ya kwana lafiya wani ko in ya ci sai makabarta idan bai sami tallafi ba saboda Allergic reaction ko borin jini, wani zai sha ruwan sanyi lafiya, wani idan yasha ba lafiya sai tari da mura. zaman lafiya ya kiyayesu, toh haka abun yake.


Toh duk wadancan canje-canjen bai dace ace sun faru ba kafin kaiwa shekarun da aka saba ganinsu. 


Domin mu a lafiyance kuma a kimiyyance abinda aka saba gani shine; fara bayyanar tasowar nonuwa tsakanin shekaru 11 da haihuwa, da kuma soma haila tsakanin shekara 12 zuwa 14 yawanci a ýaýa Mata. Inda kadan ke kaiwa 15 zuwa 16 kafin fara haila.


Yayin da duk Macen da ta kai shekaru 16 bayan bayyanar nonuwa batare da ta fara ganin haila ba hakan na nuna akwai matsala, ko kuma akaga ta kai har 15 babu bayyanar nono babu kuma haila nan ma kwai matsala, akwai bukatar a tuntubi likita.


Amma ganin yarinya da nonuwa tun daga shekaru 11 wannan duk normal ne sai dai ace ya dan yi wuri. Wasu ma nonuwan na jinkirin tasawa har sai sun rufe shekara 20 alhalin suna haila, suna da gashi a lokunan jikinsu normal amma kirjin ne kamar anjera kwai wannan ma babu abun damuwa galibi.


Menene Illar Bayyanar Saurin Balaga 


Idan alamun firikoshuyos ya bayyana toh babban mahimmin abun sani shine; Irinn wadannan yaran (Mace ko Namiji) kasusuwansu za su yi saurin kammala ƙwarinsu tun kafin lokaci yayi wanda hakan ke nuna ba za su yi tsayi ba kamar sauran mafi yawan mutane, matukar ba'a kai musu dauki ba, basa wuce tsayin kafa hudu da ďan wani abu.


Haka zalika irin wadannan yaran ka iya fuskantar ciwo na ruhi saboda damuwa, musamman wasu idan ba iyaye sun tsaya tsaye ba yan uwansu yara ka iya suke tsokanarsu ko yi musu wasan banza.



Menene Matakin Ɗauka kan Saurin Balaga

Da farko dai idan an ga haka ya dace dukkan iyaye da manya a gida su fahimci cewa wannan tangarda ce, a taimaka a sami lokaci a kaisu su ga likitan yara wato PEDIATRICIAN a babban asibiti, yayin da likitan yara zai aiki hannu da hannu da likitan sinadaran jiki ENDOCRINOLOGIST wanda dukkansu ana iya samunsu ne a manyan asibitoci wato SPECIALIST, FMC, ko TEACHING HOSPITAL ko kuma asibitocin yaran ma kai tsaye wato PEDIATRIC HOSPITAL


- Kada iyaye su jahilci wannan al'amari akai ga ganganci cewa za'a cirewa yarinya nonuwa. ko za'a nemo wani mai maganin hausa ko wanzami ya tsagasu a zare, kul da aikata hakan. Don ya rasulillahi musamman iyayen mu na karkara kar ai haka, karma afara irin wannan mugun tunanin. Shyasa nake sadaukar da lokacina domin wayar dakai. 


Ku sani wajibi ne kanku ba sai ma'aikacin lafiya ba idan kunji ana shirin yiwa irin wadannan yara aika-aika ku tsawatar. Idan kunga da gaske iyayen sun ƙi daukar shawara don Allah jeka sanar da wani babba agari, ko kuwa jami'an tsaro don tsawatarwa. 


- Kada a tsaya baiwa yarin wasu jike-jike ko magungunan shafawa a nonon. Sam babu bukatar haka.


- A zo ga likitoci kurum, idanma a asibitocin karkara ka sami irin wannan case din ka sanar dasu cewa hakane wannan abune da kunsan yana faruwa amma su yi kokari ga irin asibitin da za su je kuma za'ai abunda ya dace. A yi ta wayarma da mutanen mu, saboda yanzu matsalar ta fara yawaita. kuma hakan bai rasa nasaba da duniyar shaye-shayen tarkacen komi da komi da mata suka dorawa kansu. Domin hatta irin su hulba din nan da kuke rainawa a likitance mun san akwai estrogen cikinta. Bai kamata Mace me ciki ta rika ta'ammali dasu ba. 


- Idan an zo asibiti likitoci za su bada maganin da zai dakile cigaban saurin alamun balagar tare da bata maganin da zai hana kasusuwan saurin kwari domin su samu su cimma tsayinsu kamar sauran mutane.


- A sanya ido akan abokan wasa tare, hatta mutane daga irin wadannan yaran da tseratar dasu daga tsokana ko cin zarafin mutanen banza cikin al'umma, domin da za'a sadu dasu zasu dau ciki kai tsaye, ko da jaririya ce kuwa ta sami wannan yanayin inda za'a saka mata ruwan halittar namiji ciki zai iya shiga bare wanda suka tasa. Don haka alura.


Fatan Bayanin ya ilmantar.


[Ibrahim Y. Yusuf]



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post