Abubuwan da ya dace ku sani gameda HANTA — Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Abubuwan da ya dace ku sani gameda HANTA — Android Pols

Abubuwan da ya dace ku sani gameda HANTA
Abubuwan da ya dace ku sani gameda HANTA 


Hanta a yaran likitanci ana kiranta da "LIVER" .

Hanta na ɗaya daga cikin sashin jikin ɗan adam masu muhimmanci wajen inganta lafiyar jiki da samun daidaito ga sassan jiki.


Hanta itace mafi girma a cikin ɗan adam, tana daga sama ɓarin dama na ciki daga ƙasan murfin ciki.


Hanta ita ke sarrafa abinci, tace magani, samar da sinadarin carbohydrates, protein da fats.


Aiyukan hanta a jikin ɗan adam sune kamar haka.


1. Hanta na tace sinadaran guba da gurbatattun abubuwa daga cikin jini.

2. Samar da ruwan maɗaciya wanda ke taimakawa wajen narkar da kitse.

3. Hanta na canza glucose zuwa glycogen don ajiya daga baya ta sake maida shi glucose idan jiki ya bukata.

4. Hanta na taimakawa wajen narkar da kitse da kuma sarrafa cholesterol.

5. Hanta na samar da muhimman furotin (Protein) kamar su albumin da kuma sinadaran da ke taimakawa wajen haduwar jini.

6. Tacewa da kuma rushe ko ragargaza magunguna da sauran sinadarai da aka sha.

7. Samar da sinadaran daskarar da jini lokacin da aka ji rauni domin tsayar da zubar jini.

8. Hanta na samar da sinadaran da ke taimakawa wajen kare jiki daga kamuwa da cuta.

9. Sarrafa da daidaita matakan hormone daban-daban d.s.s.

10. Hanta tana da matukar muhimmanci a cikin jikin mutum saboda wadannan ayyuka da take yi, wanda idan aka rasa, zai iya haifar da matsaloli da dama ga lafiyar jiki.


© Ibrahim Abubakar zakari


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel