Abubuwan Da Suke Jawo Rashin Inzali Ga Maza A Yayin Da Suke Yin Jima'i Da Matan Su |
Akwai wata matsala da ke tasowa wacce ke damun maza, matsala ce wacce ya kamata ayi bayanin ta tare da abubuwan dake haddasa ta da kuma hanyoyin samun mafita.
Wannan matsala itace ta maza masu sabon aure, mutum yai aure wata 1 zuwa 2 a lokutan da yake saduwa da iyalin sa sai yaji ya kasa yin inzali. Wato ba zai iya kawowa ba sai dai yai ta yin jima'i har ya gaji ya tashi ba tare da maniyyi ya fita daga gabansa ba.
Wannan matsala tana damun maza domin muna yawan samun sakonni akan hakan. Shiyasa muma muka tuntubi masana lafiya wadanda suke da kwarewa a wannan fagen domin su kawo muku mafita akan wannan matsalar.
Sai dai abin mamaki lokacin da za kaji wasu mazan na korafin cewa basa iya yin inzali wasu kuwa sai kaji suna cewa basa yin inzali gabaki daya, wannan ne damuwar su. To masana dai Kamar yadda suka bayyana mana akwai wasu abubuwa dake jawo namiji ya kasa yin inzali a yayin da yake gudanar da jima'i da matarsa.
(1) Amfani da kwayoyi na kara karfin gaba, wato akwai mazan da suke yin amfani suna shan wasu kwayoyi domin su dauki tsawon lokaci ba tare da sun kawo ba. Ko kuma yin amfani da wasu magungunan domin samun karfi idan ana saduwa.
To yin amfani da irin wadannan kwayoyi na jawo maniyyi mutum ya tsotse wato ya kone. Amma kai ba za ka gane hakan ba saboda kai baka san illar da shan wannan kwayoyin ke yi a jikin ka ba. Kuma wasu mazan sun saba yin amfani da wannan kwayoyin, don haka dole ne a kiyaye.
(2) Yawan motsa jiki akai akai-akai, shima masana lafiya sun yi bayani akan wannan inda suka bayyana cewa motsa jiki a yawancin lokuta yana haifar da daukewar maniyyi, wato idan yaje yin saduwa da iyalinsa sai yai ta yi amma kuma ba zai fitar da maniyyi ba.
Amma fa anan ba wai ana nufin kada mutum ya dinga motsa jikin sa ba. Kamar 'yan kwallo za ka samu suna motsa jiki ko masu aikin kaki to ba irin wannan ake nufi ba, ana nufin wanda a koda yaushe ba shida wani aiki sai motsa jiki safe da dare.
(3) Yananyin waje, ma'ana wanda suke rayuwa wajen zafi ko wajen da yake mai sahara ne kuma idan mutum bai damu da yawan shan ruwa ba. Shi ruwa babu abinda ya kaishi aiki a jiki dan adam.
Shi ruwan idan mutum zai yawaita shan sa duk cutar dake jikin mutum za kaga yana samun sauki. Masanan suka ce idan mutum ya samu kansa a waje mai zafi kuma baya yawan shan ruwa to yakan jawo masa karancin fitar maniyyi a yayin da yake saduwa da iyalinsa.
(4) Rashin zakuwa a yayin saduwa, yawancin maza masu sabon aure za ka samu ba su saba yin jima'i ba kuma ba neman matan banza suke yi ba. To galibi idan suna jima'i ba su fiya yin inzali ba saboda rashin sabo. Amma idan an kwana biyu suna yin jima'i zai zama sun saba.
Wannan sune kadan daga cikin abubuwan da masana suka bayyana wanda ke jawo rashin yin inzali a yayin da suke yin jima'i da iyalin su.
Nan gaba za mu kara fadada kawo muku wasu daga cikin dalilan da masana suka bayyana da suke jawo wannan msataloli na rashin fitar da maniyyi a yayin saduwa.