Abubuwan Da Akeso Maijego Ta Yi Amfani Dasu Da Zarar Ta Haihu Da Kwana 7 — Android Pols

Abubuwan Da Akeso Maijego Ta Yi Amfani Dasu Da Zarar Ta Haihu Da Kwana 7
Abubuwan Da Akeso Maijego Ta Yi Amfani Dasu Da Zarar Ta Haihu Da Kwana 7


Domin ƴan uwan mu kuma iyaye mu mata musamman waɗanda suke haihuwa. Sau da yawan lokuta za kaga idan mace ta haihu ba ta kulawa da jikin ta babu gyara wanda zai dawo da martabar jikin ta, ko kuma don maigida ba zai neme ta bane a wannan lokacin. Hakan ke jawo kaga mace duk ta canja ta zube. Daga wannan lokacin idan baki gyara ba sai kaga mace duk ta lalace.


Daga baya kuma sai kaga mace tazo tana ta tambaya cewa tana buƙatar maganin da za ta yi amfani dashi domin samun lafiya. Abinda ya kamata mata kusani shine duk lokacin da mace ta samu haihuwa to jikin ta yana canjawa cikin sati 1. Shiyasa akeso idan kin haihu to kada ki zauna kawai kibar jikin ki haka, akwai abubuwan da yakamata kiyi amfani dashi da zarar kin haihu da sati 1.


Wasu matan idan sun haihu idan ka tunkari ɗakin su za kaji suna ƙarni ko ɗoyi duk a dalilin rashin kula da rashin gyara jiki. Anaso idan mace ta haihu da kamar sati ko sati 2 ta dinga yin amfani da kayan gina jiki wanda zai ƙara mata lafiya ita da jaririn ta. Kayan marmari irin su kankana, gwanda, ayaba, lemon zaƙi da abarba da sauran kayan marmari makamancin su.


Anaso mai jego kullum ta ringa cin irin waɗannan kayan marmari ko ba duka ba a ƙalla dai ko guda 3;ne ki ringa ci a rana ba sai kinsha kowanne ba, domin ba kowace mace ke da halin siyas ba. Amma idan kinada hali ko kuma mijinki yana da ikon ya dinga siya miki a kullum to lallai yana da kyau ki ringa shan su domin zakiga amfanin su a jikin ki.


Sannan kuma anaso maijego ta maida hankali wajen shan abubuwan da zasu ƙara girman nono da kuma ƙarawa nonon ruwa wanda shi kansa jaririn zai samu ƙarin lafiya da isasshen nonon. Ki yawaita yin kunun alkama kina sha, idan da hali kullum ki ringa yi kina sha ko kuma duk bayan kwana 2 kiyi.


Haka kuma anaso maijego ta yawaita cin dabino, aya da kwakwa suma waɗannan abubuwan suna daga cikin wanda suke ƙarawa mace lafiya da kuzari, kuma zai inganta lafiyar jaririn na ta. Sai kuma akwai abinda maijego za ta ƙara maida hankali akai na ɓangaren gabanta. Anaso ki ringa tafasa garin lalle kina yin tsarki dashi. Ko kuma ki samu garin lalle da bagaruwa ki tafasa kina tsarki dashi.


Haka kuma yana da kyau maijego ta ringa amfani da tsumi na mata wanda zai gayra gaban ta ta fitar mata da dukkan wani datti ko ciwon sanyi. Kuma ki ringa shan zuma a kullum kamar sau 2 a rana za ta taimaka miki wajen ƙaramiki lafiya da kuma wanke miki ciki. Wannan sune abubuwan da yakamata ki maida hankali akai da zarar kin haihu da sati 1 ko 2.


Domin yin waɗannan abubuwan za su taimake ki wajen dawo da martabar ki ta ƴa mace, kuma za su ƙara inganta miki lafiyar ki tare da abinda kika haifa. Ki yawaita yin su har zuwa lokacin da zaki arba'in. Amma ba munce dole sai kinyi duk waɗannan abubuwan ba domin ba kowane yake da halin siya sa sai kuyi daidai gwargwado wanda zaku iya.


Akwai matan da jini yana iya ɗauke musu tun kafin kwana 40 to idan jini ya ɗauke kuma kinga maigida zai kusance ki ne, idan kuma ya kusance ki bakida ni'ima kinga akwai matsala, shiyasa muke sanar daku abubuwan da yakamata ace kunyi domin dawo da ƙimar ku.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post