Abubuwan Da Akeso Mace Tayi Yayin Da Mijinta Ke Saduwar Aure Da Ita |
A duk lokacin da namiji yake tarayya da iyalinsa yawancin mata basa iya yin komai sai dai su kwanta kamar wani dutse babu wani abu da za ta yiwa mijin sai dai kawai ya biya buƙata ya tashi, to duk macen dake yiwa mijin ta hakan za suyi ta samun matsala ne. Ita ma kuma a nata ɓangaren bata jin wani daɗi a zuciyar ta, shi kuma a tunanin sa kawai bataso ne ko kuma bata jin daɗin sa. Ba kowane namiji ne zai yi wannan tunanin ya gano cewa matata ba ta jin daɗi bari nayi abinda za ta ji daɗi.
Irin wannan matsala yawancin mata suna fuskantar ta wato rashin jin sha'awa a yayin saduwar aure. Mun sha yin bayani akan abubuwan dake jawo mace taji ba ta jin sha'awar yin jima'i da mijin ta. Mun ce akwai irin yadda shi kansa mijin na ta ya horar da ita da jima'i. Wasu mazan suna yin jima'i da matar su a kullum kamar sau 2 wasu kuwa sama da haka, wasu mazan sai su yi kwana 2 ko 3 ko kuma sama da haka ma ba tare da sun kusanci matar su ba, don akwai wanda kwanakin baya muna hira dashi yace min wani lokacin yana yin sati bai kusanci matar sa ba.
To ita sha'awa dasata ake yi, yawan yadda mutum ke kusantar matarsa yawan yadda za ta ji tana sha'awar sa a koda yaushe. Sai dai kuma akwai wasu matan wanda su haka Allah ya halicce su basa jin wata sha'awa ba su san menene sha'awa ba. Duk irin yadda zaka taɓa su ko kuma kayi musu wasa ba za su san ana yi ba domin haka Allah ya yi musu halittar su. Kuma duk irin maganin da za su yi amfani dashi sai dai kawai su kashe kuɗin su a banza domin babu wani canji da zasu gani haka Allah yake so su zauna.
Wasu matan kuma matsala ce ta sanyi wacce ke kashe musu sha'awa kawai sai suji sun daina jin wata Sha'awa a yayin saduwar aure. To idan matsala ce ta cutar sanyi ya jawo miki ɗaukewar sha'awa to kiyi ƙoƙari ki nemi magani. Idan kuma dabi'a ce yadda mijinki ya saba yi miki to kiyi ƙoƙari kisa ya canja. Domin yawancin maza idan za su sadu da iyalin su basa fara gabatar da yin wasanni wanda zai motsawa da mace sha'awar ta kawai haka za su afka mata su biya buƙatarsu su tashi. To yin hakan babban kuskure ne kuma idan miji ya saba yiwa matarsa hakan to fa zata kasance ba ta jin sha'awar ko kaɗan.
Abubuwan Da Akeso Mace Tayi Yayin Da Mijinta Ke Saduwar Aure Da Ita
Ana so idan miji zai kwanta da iyalinsa to yai aƙalla minti 20 yana yi mata wasa wanda yin hakan zai motsa mata sha'awa, kuma a yayin wannan motsa sha'awa mace takan iya gamsuwa da kaso 30 cikin 100. Don haka kiyi ƙoƙari kisa ya fara yi miki wasanni a duk sanda yazo yin saduwar aure dake. Kar kiji kunyar nuna masa hakan domin mijinki ne kuma kinada haƙƙi yai miki hakan. Kuma ba kowane namiji ne yake da tunanin cewa idan yaiwa matsar wasanni za ta ji daɗi ta gamsu ba.
Anan shawarar da zan baki shine kiyi ƙoƙarin ki nuna masa abubuwan da yakamata yai miki wanda zakiji daɗi sannan kuma idan yana saduwar aure dake koda baki jin daɗin to ki nuna masa kinajin daɗin domin hakan zai ƙara masa himma. Anaso idan mijinki yana saduwa dake ko bakya jin daɗin ki ruƙuƙunƙume shi ki matse shi. Sannan kuma ki ringa yin sheshsheƙa wato irin wannan surutan da mata suke yi idan sunji daɗin saduwa.
Sannan kuma idan yana saduwar aure dake ki ringa miƙe kafafun ki da hannayen ki suna harbawa wanda zai tabbatarwa da mijin naki cewa kinajin daɗi, sannan kuma ki yaba masa ki gode masa. Kalamai dai na nuna cewa kinji daɗi. A ƙarshe su kuma maza su ji tsoron Allah wajen tabbatar da sun sauke nayin iyalin su. Kuma dole ne maza su tsaya tsayin daka wajen magance matsalar iyalan su.