Abubuwa Uku Game Da Tsaikon Warkewar Targaɗe - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Abubuwa Uku Game Da Tsaikon Warkewar Targaɗe

Abubuwa Uku Game Da Tsaikon Warkewar Targaɗe
Abubuwa Uku Game Da Tsaikon Warkewar Targaɗe


Targaɗe rauni ne ga tantani da ke riƙe ƙashi da ƙashi a gaɓa. Wannan rauni kan kasance sakamakon murɗewar ko ɗamewar gaɓa fiye da ƙima yayin gudanar da ayyukan yau da kullum, wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, da sauransu.


1. Targaɗe na da matakan tsanani kamar haka:


Matakin farko: Tantanin zai samu rauni saboda ɗamewa ko talewa fiye da ƙima.


Mataki na biyu: Tantanin zai samu rauni saboda 'yar yagewa ko tsagewa.


Mataki na uku: Tantanin zai tsinke ne gaɓa daya.


Saboda haka, warkewa daga raunin targaɗe ya dogara ga tsananin raunin da tantanin ya samu.


2. Tantanin da ke riƙe ƙashi da ƙashi, saɓanin tsoka, ba shi da jijiyar jini kai tsaye da ke kawo masa sinadaran abinci, magani da sauran sinadaran da jini ke ɗauke da su.


Saboda haka, lokacin warkewar raunin tantani kan ɗauki makonni har zuwa watanni gwargwadon tsananin raunin.


3. Rashin samun kulawar likita da kuma bijire wa ƙa'idojin da likita ya gindaya, musamman dangane da matakan kariya yayin jinyar raunin, da kuma ƙayyade ranar da ya kamata mutum ya fara taka ƙafar, ko kuma ya koma wasanni.


Domin sau da yawa, 'yan wasa kan koma wasa ba tare da cika makonni ko watannin da likita ya ɗiɓa musu ba. Wanda hakan kan sake ta'azzara raunin kafin ya warke.


Wannan hoto na nuna tantanan da ke gaɓar idon sawu da tafin sawu ne.


© Physiotherapy Hausa


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel