Abubuwa da ya dace duk namiji ya Sani Game Da Mace
![]() |
Abubuwa da ya dace duk namiji ya Sani Game Da Mace |
Maza ku gane, lokuta da dama in kun ga muna wasu 'yan hali haka da qorafi irin ka share ni, ba ka nemana yanzu, baka damu dani ba, ka bar so na, baka da lokacina yanzu, banda wani muhimmanci a wajen ka, etc.
Qaunace ke samu irin haka, da kewar ku (because we really miss feeling connected to you).
Ku sani abu 3 muke buqata
1. lokacin ku,
2. kulawar ku da
3. Lallashin ku.
Abunda ya kamata kuyi shine
1. Kirata a waya, ko kaje ka sameta ko ku zauna.
2. Bata hakuri
3.Tambayeta me ke damunta
4. Barta tayita zubanta ( naturally da mun furta muku abunda ke ran mu mukan yi feeling relieved)
5. Lallasheta ka fada mata uzurin ka
6. In matarkace jawota ka rungumeta fadamata "kin san kima da matsayinki a wajena yafi ta kowace mace. Qaramata da sugar har da garin madara.
7. Bata kyauta komin qanqantanta, ko tura mata 'yar alert kace ta kace ta ajiye a asusunta(badole bane).
Shikenan ka kashe wata 'yar matsala ta watanni a gidan ka.
Washe gari hatta takunta sai ya chanza, infact har suna zata chanzama.
Yeah we are that simple.
✍️ Fatimah Chikaire
Leave Comments
Post a Comment