Abin sha mai kara kuzari (Energy Drink) na farko a duniya
![]() |
Abin sha mai kara kuzari (Energy Drink) na farko a duniya |
Abin sha na mai kara kuzari (Energy Drink) na zamani na farko ya samo asali ne a kasar Japan bayan gama yakin duniya na biyu. Abin sha na farko mai kara kuzari shi ne Lipovitan D, wanda kamfanin Taisho Pharmaceuticals ya samar a shekarar 1962. Lipovitan D wani abin sha ne na ganye da ake sayar wa ma'aikatan masana'antu da direbobin manyan motoci. Ana sayar da shi a cikin ƙananan kwalabe. An yi shi don haɓaka ayyukan tunani da na jiki. Babban sinadarin da ake hada shi, shi ne (Taurine), wannan wani sinadari ne a da ake hadawa a cikin Red Bull (wani abinsha mai kara kuzari).
Matsalolin (Energy Drink)
Cututtukan da suka shafi jijiya: Abubuwan sha masu kara kuzari (Energy Drink) na iya ƙara hawan jini, bugun zuciya, da numfashi. Hakanan suna iya haifar da rashin natsuwa, da rashin barci. Kana kuma su na iya kai mutum ga shanyewar barin jiki da matsalolin gudawa.
Abubuwan sha masu kara kuzari (Energy Drink) na iya haifar da munanan al'amuran zuciya da jijiyoyin jini da bugun jini. Da ciwon kai da yawan hasala. Sannan suna iya zama jaraba (addictive). Wanda ya jarabtu da shan sa, idan bai sha ba baya iya aiki yadda ya kamata.
Wasu masana sun ba da shawarar cewa mutane su guji shan (Energy Drink) akai-akai, musamman tare da barasa. Har ila yau, sun ba da shawarar a kafa Dokoki don iyakance sayar da abubuwan sha masu kara kuzari, musamman ga kananan yara.
Leave Comments
Post a Comment