ABIN DA YAKE KASHE MATANMU NA HAUSA A ZAMANTAKEWAR AURE - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

ABIN DA YAKE KASHE MATANMU NA HAUSA A ZAMANTAKEWAR AURE

ABIN DA YAKE KASHE MATANMU NA HAUSA A ZAMANTAKEWAR AURE
ABIN DA YAKE KASHE MATANMU NA HAUSA A ZAMANTAKEWAR AURE 



Na dade ina irin wannan nazarin game da rayuwar matan kasar hausa akan menene dalilin da yasa suke saurin tsufa da zarar an yi musu aure sun je gidan miji.


Za ka ga yarinya karama wacce aka haifeta a gabanka da zarar ta isa aure an kaita dakin miji shekara daya kawai zuwa biyu bayan ta haihu idan ka ganta abin zai baka tsoro da mamaki domin zaka ganta duk ta tsufa ta yank'wane kamar wata Anty.


Abin da yake bani mamaki shine kafin 'yan matan su yi aure sun iya kama jikinsu da daukar wanka da kwalliya. Watakila wannan shine dalilin da yasa samari suka yi mata chah a lokacin tana gidansu. Amma da zarar ta shiga dakin miji shikenan wannan kama jikin da wannan wankan da kwalliya duka sun zama tarihi. 


Musamman idan ta samu juna biyu ko kuma ta haihu a wannan lokacin wata matar ko abincin da ta dafa wani namijin mai tsantsami ba zai iya ci ba balle har yayi hira ko hada shimfida da ita ba. Kuma a irin wannan yanayin ba kowane namiji bane zai iya zama da irin wadannan matan ba dole sai dai cikin biyu ayi daya ko dai ya saketa ko kuma ya karo aure. 


Da yawa matanmu haka suke basu damu da ado da gyaran jikinsu ba kamar yadda suke a lokacin suna 'yan mata. Dalilin kenan da yasa mazajensu ke gudunsu suna bin' yan matan waje ko karuwai. Domin matansu basu yi musu irin wannan kwalliyar da suke gani a wajen 'yan matan waje. 


Kullum zaka tarar da mace da daurin kirji kai a chukurkud'e ya tsufa ba kitso ba sarta. Yadda take a hargitse haka 'ya'yanta da d'akinta da gidanta suke babu kulawa. Idan mijin yayi magana domin ta gyara sai tace: "Kawai dai Baban Auwal ka gaji da ni ne duk shi yasa kake ta yimin irin wannan tsangwamar... To ya kake son nayi ni inji ce da zanyi ta aiki ba na gajiya? Jiya fa nayi wanka kuma na share d'akin nan sannan nayi wa yaran nan wanka".


Babu yadda mijin ya iya dole sai dai yayi hakuri ya daina gayyato abokansa gidan dan kada su fahimci matsalar matarsa ko kuma ya fara tunanin sakinta ko kara aure. 


Abin da zai baka mamaki shine irin wadannan kazamen matan idan suka tashi fita unguwa wallahi idan ka gansu ba zaka iya ganesu ba... Wanka suke dauka ayi kitso da k'unshi da gyaran jiki kamar za ta je gasar kyawawa. Har kananen 'ya' yansu sun gane su da zarar sun yi kwalliya to unguwa za'a tafi sai ka ga yaran sun fara binsu suna yi musu kuka dan kada iyayen su tafi su barsu a gida.


Idan kuma aka yi rashin sa'a mazajen suka gaji suka sakesu idan suka fara zawarci sai kuma kaga sun fara wanka da kwalliya. Wasu mazajen kuma zasu daukesu a rashin sani sai anyi auren kuma hali ya bayyana a sake sakinsu. To haka za'ayi tayi har ma qarshe su rasa wanda zai auresu.


Wallahi mata wannan shine babbar matsalarku shi yasa kuke tsufa tun da kananen shekarunku. Kuma shi yasa mazajenku ke gudunku ko aurenku ya mutu... Ku lura da kyau ku ga yadda turawa, larabawa, indiyawa da qabilunmu wadanda muke zaune qasa daya ku gani haka suke yi?


To dan Allah mata a daure a dinga wanka da kwalliya da tsafta domin ba kowane namiji bane zai iya zama da qazamar mace irin wannan ba. Kamar yadda kuke gyara jikinku kafin aure dan samari su gani su yaba haka yakamata ku gyara jikinku a gidajen mazajenku domin aurenku yayi lasting kuma ku zauna lafiya. Jikin mata ba irin na maza bane dole sai da gyarawa.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel