Zuwa gareku Maza Da Sabbi Angwaye |
Wani ne ya turomin saƙo akan zaiyi aure yana neman shawara da "dos and dont" na aure. Shine naga ya dace in yi posting domin nasan akwai waɗanda zasu amfana, duk da nasan abune mai wuya cikin dan ƙanƙani lokaci da rubutu a fadi abunda ke cikin aure tunda wani abun sai ka shiga zaka gani ko ka gane.
Ga shawarwarin da na bashi kamar haka
1. Ka sani aure ibadane a cikin dukkan ibada da ruyawar akwai jarrabawa a cikin, hakuri, kiyaye dokokin Allah da koyi da sunnan Annabi zai kaika ga cin nasara a ciki.
2. Ka sani Amanace a wajen ka kuma Allah zai tambayeka akan amanar da aka damƙa maka.
3. Iyayenta sun baka ita ne dan kyautata zato a gareka akan ƴar su zata samu kuluwa da farin ciki a wajen ka, sabida haka ka zama gatanta, karka sake ka samarmata da akasin haka domin zai nuna gazawarka da ƙasƙanci a matsayin ka na jagora.
4. Kiyaye dukkan haƙƙokinta da ya rataya akan ka. Dole ne ka kiyaye tare da yin dukkan abinda ya dace wanda shari'a ta ɗora maka.
5. Ka sani ita mace da kyauta da kyautata mu'amala aka fi sace zuciyarta, ka kasance mai kyautatawa a cikin kalamanka wajen yi mata gyara da kiyaye furta abunda zai cutar da zuciyarta, ka kyautata a cikin ciyarwa, tufatarwa, mu'amalantarta da 'yan uwanta.
6. Ka sani mace halittace mai taushin zuciya da raunin hankali, wani lokaci zakaga abunda kake so wani lokaci sai kayi hakuri matuƙar hakuri da kawaici da ita.
7. Ka sani kai jagora ne a gidanka dan haka dole ka kasance abun koyi a cikin dabi'u da halaye. Kar ka bari munanan dabi'un ka ya zama abun kyama da zargi a cikin gidan ka, matuƙar baka kiyaye naka ba zaiyi matuƙar wuya ta iya kiyaye nata, wadda yin hakan zai zama silar fititintunu a auren ku.
8. Kiyaye tsabtar jikinka, babu wadda yake son kusantar ƙazamin mutum, ka kasance mai kiyaye tsabtar jikinka a duk lokacin da zaka kusanci matarka, wannan zai samar mata da nitsuwa a zuciyarta da zata mu'amalance ka cikin kwanciyar aurenku cikin sauqi. Bayan tsabta, askin sama da ƙasa da yin brush atleast safe da dare, Ka riqe turare dan shine zai zama dan saƙonka zuwa ga matarka cikin sauƙi.
9. Ka kiyaye shigan 'yan uwanka al'amuran rayuwar gidan ka ko tsakaninka da matarka, cikin sauqi in baka iya tsayarda kowa a matsayar sa ba za'a dagulama lissafi da rayuwar gidanka ba akan abunda bai kai ya kawo ba a hanaka zaman lafiya da jin dadi da iyalanka.
10. A duk lokacin da kuka samu matsala ka bada kofar zama tattaunawa a tsakanin ku domin shine kofa mafi sauƙin samu gyara, mafita da maslaha a tsakanin ma'aurata.
11. Matarkace, ka karanceta kasan waye ita da yadda take mu'amalantar mutane, Karka bari wani ko wasu su zo suna fadama waye matarka domin akasarin lokaci ƙarya ko sharrinta za'a fadama ba alkhairintaba.
12. Ka sani a cikin zamanku zakaga abunda baka so a game da ita, ka tuna itama haka zata gani akan ka, so kuyi hakuri akan wadannan ku na yawan tuna kyawawan halayen juna dan su zasu kasance abunda zasuna kawar muku da wadanchan munanan halayen.
13. Ka kasance mai kawaici kuma mai gyara a cikin gidanka ba mai dagula lissafiba.
14. Ka sani namiji mai wasa da raha da iyalansa yafi samun walwala da jin dadi a cikin aure fiye da miji mai tsare gida.
15. Ka kasance mai iya bada hakuri in kayi ma matarka kuskure domin yafi sauƙi kuma yakan karya lagwan fitintunu da dama a tsakanin ma'aurata.
16. Ka sani yadda kake da haƙƙi akan matarka wajen kwanciyar aure haka take dashi akan ka, karka kasance marowaci ko mai kauracewa matarka ba tare da dalilin da musulunci ya tanadar ba dan akwai cutarwa a ciki sosai, kuma kofar bude fitinane sosai a aure da rayuwa duka.
17. Ka zaman to da ita abokiyar shawara ko da kuwa ba lallai kayi aiki dashi ba, yin hakan zai baka damar sanin irin hankali da tunaninta wadda hakan zai baka damar mata gyara a cikin tunanin ta.
18. Ka zamto mai iya amsan uzuri domin shi dan adam ajizine mai kuskure ne, kai ma zaka iya kuskure kuma zaka so tama uzuri. Kuma yin uzuri ma juna yakan rufe kofofin fitintunu da dama a aure.
19. Ka sani waya (phone) da social media yana daga cikin babban ƙalubale da barazana da aure da dama ke fuskanta yanzu, ta kashe aure ta gusar da zaman lafiya a gidaje da dama, kayi taka tsantsa wajen kiyayewa.
20. Ka sani zaku iya gamo da jarrabawa kalala a cikin aurenku; na dukiya, rashin lafiya, yara, haihuwa, makota, iyaye, 'yan uwa, abokai, abun hawa, kasuwanci, karatu, aiki, tafiya da sauran su.
20. Ku riƙe Allah ya zama abun dogaro a cikin rayuwar ku dana auren ku, ka sani a duk lokacin da kuka bar Allah acikin al'amuran ku zai barku da wayo da wayewarku ne wajen warware matsalolin ku wadda ni da kai duk mun sa bin wayo da wayewa bata bullewa kowa.
21. Ka zama mai sirri da samun na gaba dashi wajen neman shawara, Karka taba zama cikin 'yan "hide my Id" 99% din su basa samun mafita face baki da suke jawoma kan su da lalacewar auren su.
Wannan kadan ne daga cikin abunda zan iya fadama kasancewar tsawon rubutu.
Ina mai muku fatan alkhairi da zaman lafiya a cikin auren ku.
Fatimah Chikaire