Zamantakewar Aure — Matarka Sarauniyarka |
❝Ka riƙi matarka a cikin gidanka tamkar wata sarauniya, kada ka maisheta tamkar wata baiwa a cikin gidanka wacce ba ta da wani amfani a wajenka da ya wuce ta biya maka buƙatarka a lokacin da ka buƙace ta. Kubi salo na jin daɗin soyayya a zamantakewar aurenku, ku haifarma da kanku farin ciki mai ɗorewa a tsakanin ku, kada wani sashe ya muzgunawa wani sashe a tsakaninku. Ku mutumta juna, ku ɗebe ma junanku kewa, hakan shi ne zai sa kuji daɗin aurenku ta re❞
"Wasu mazan sukan nuna maƙurar soyayyarsu ga ƴan matansu kafin su aure su, amma da zarar anyi auren an ɗauki tsawon lokaci sai kaga wannan soyayyar ta ragu ba tare da matan sunyi musu laifin komai ba"
"Zaiyi matuƙar wahala kaga mace tana matuƙar son ka kafin kuyi aure, bayan auren kuma ta daina nuna maka soyayya, sai dai idan kaine ka fara nuna mata hakan. Mata sukan ririta mazajen su a gidan auren su fiye da yadda mazan suke nuna ta su soyayyar ga matayen su"