Yadda zaki kara girma, gyara da cikowar nono cikin wata daya

Yadda zaki kara girma, gyara da cikowar nono cikin wata daya
Yadda zaki kara girma, gyara da cikowar nono cikin wata daya 


Duk macen da ke bukatar karin girma, gyara ko cikowar nono ga maganin da ya dace ku yi amfani da shi insha Allah za'a samu biyan bukata 


Maza da yawa suna son suga kirjin mace ya ciko ya tsaya yayi kyau ko babu komai akwai kyawon gani, wasu kuma basu damu da wannan ba. Amma da yawa maza suna son nono sosai domin yana da nashi rawar da yake takawa a wajen kwanciya yayin wasanni.


Sannan yan mata da yawa suna samun kalubale daga samari idan suna da kananan halitta na Nono, wasu kuma da auren nasu amma sun bari nono su ya zube ya lalace ya zama babu kyawun gani har ta kai ya daina birge miji da daina bashi sha'awa. 


Wata macen nonon ta yana zubewa ne a dalilin haihuwa, amma kuma idan ana kula dashi ba zai zube gaba daya ba. Wasu matan haihuwar bata wuce daya ko biyu amma idan ka ga nono ta tamkar wata uwar marayu duk ta bari sun zube sun lalace.


Yadda zaki kara girma, gyara da cikowar nono cikin wata daya 


Ga hanyar da zaki bi domin gyarwa tare da kara musu kyawun gani.


Abubuwan da zaki Nema, sune kamar haka:


1. Garin plantain (Filenten) gwangwani 2 da rabi. 

2. Garin hulba gwangwani 1.

3. Farar Shinkafa ta tuwo gwangwani 1.

4. Gyada rabin gwangwani. 


Dukkan su zaa hade su waje daya a dake su sosai sanan a rika salala (kunu)dashi a rika sha da safe kafin a karya zuwa wata daya.


Insha Allah wannan hadin bayan gyaran Nono da yake har gyara jiki yake da karin kiba wajen gyara jiki. Duk wacce take son girma, gyara ko cikowar nono idan tana yin wannan hadin za ta samu biyan bukata. 


Allah yasa mu dace.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post