Yadda Zaka Gane Sayyadar Gaske (Mata Ta Gari) |
Idan kana burin auren mace masoyiyar Annabi ﷺ wacce zaku zauna lafiya bisa koyarwar addini kuma ta tarbiyantar maka da yara a wannan tafarkin, to ga hanyoyin da zaka bi domin banbance Sayyada yar Media da Sayyadar Gaske.
Da farko, ganin sayyada a filin maulidi ko wurin majalisin sha'irai ko tana yawan daura abubuwan addini a Media, wannan alama ne mai kyau akan cewa masoyiyar Annabi ﷺ ce, Amma akwai abubuwan dake cika soyayya, domin sau tari zaka samu mutum a cikin sha'anin soyayya amma sai zama ya haɗa ka dashi zaka gane yana dai son abin so amma baya koyi da abin so.
Bayan ka same ta da soyayyar Annabi ﷺ, to ka binciki sha'anin neman ilimin ta na addini, shin tana zuwa islamiyya sosai, meye matakin karatun ta, idan kuwa bata zuwa, ka bata shawarar komawa ko kuma ka mayar da ita ka dauki nauyin karatun.
Idan bata zuwa islamiyya sosai ko bata zuwa kwata-kwata, sannan kuma kace ta koma bata koma ba, wallahi zaman aure da ita bisa tsarin addini zai yi wuya, wasu abubuwan gani zata yi kana da takura da iya-yi.
A wannan zamanin da muke ciki, gara ka hadu da yarinya tana dawowa daga islamiyya ka nemi soyayyar ta sannan ka koya mata son Annabi ﷺ da zuwa maulidi, akan ka hadu da yarinya a gun maulidi amma bata kulawa da ilimi.
Ana cikin wani zamani ne yanzu da iyaye da yanmata mafi yawa basu damu da ilimin addini ba, masu kokarin sune suke saukan Alqur'ani ko suyi hadda, amma hukunce-hukuncen addini basu damu dashi ba, iya karatun Alqur'ani kuwa baya fahimtar da mutum menene addini, shi kuwa aure duk wanda bai fahimci addini ba, adalci zai mai wuya, idan mace ce, biyayya zai mata wuya.
lokaci yayi da za'a ajiye soyayya a gefe a dauki abubuwa masu muhimmanci a auna a mizani, Allah ya datar damu ya hadamu da mata nagari.