Yadda ake ƙara girman hips cikin sauki — Android Pols

Yadda ake ƙara girman hips cikin sauki — Android Pols
Yadda ake ƙara girman hips cikin sauki


Ina masu neman karin ‘Hips. ’ Ina son a fahimci cewa girman kugu ko hips halitta ce, wasu matan har kauce hanya suke yi, su je a saka musu ƙugun roba. Kun ga akwai alamar kauce hanya a nan ke nan. Akwai nau’in ababen da mace za ta rika ci, sannu a hankali, kyan diri da halittarta za su kara fitowa, ita ma za ta rika ji ta kara cika, ta yi kyau.


Yadda ake ƙara girman hips

Akwai hanyoyi da dama na yadda ake ƙara girman hips da Masana a wannan fannin suka bayar da shawarwarin amfani da waɗannan abubuwan kamar haka:


  • Abarba, 
  • Ayaba, 
  • Gwanda, 
  • Kankana, 
  • Zuma, 
  • Madarar ruwa. 


A kan hada su waje guda, a markada su, har sai sun zama ruwa, sai a ɗan kara zuma da madara. Bayan wannan, mace za ta rika sha a koda yaushe. Haka kuma kina iya samun Zogale dafaffe, ki hada da ganyen Alayyahu, ki zuba Tumatiri da Albasa, ki yi kwadonsu, ki rika ci. Haka nan za ki rika yin wadannan kayan lambun da ki ka markada, sai ki rika sha misali da asuba ko da sassafe kafin ki fara cin komai, Insha Allah za'a samu ƙarin hips yadda yadace.


Yadda ake ƙara ni'ima 

Dangane da bayani kan abubuwan ni’ima. Kamar kullum mukan bayyana cewa mata su yawaita amfani da waɗannan abubuwan kamar haka :


  • ruwan Rake, 
  • ruwan Kankana, 
  • ruwan Kwakwa, 


Sai a matse su, a hade ruwan guda. Ki rika sha so uku-uku a rana.


Uwargida, kina iya yin wani hadi na musamman, wanda shi kansa maigida zai iya amfani da shi, hakan ma yana ƙara danƙon soyayya da fahimtar juna. 


Yadda ake ƙara ni'ima 

Misali, ki samu waɗannan abubuwan:


  • Alkama, 
  • Danyar Gyada,
  • Waken Soya,
  • Aya, 
  • Madarar ruwa,


Sai ki jika ki markada su, ki tace, idan ya zama gasara sai ki rika damawa kamar yadda ake dama Koko, sai ki zuba madara ta ruwa, ki yi kamar sati biyu kuna sha. Da yardar Allah za a dace.


Haka kuma ga wadanda suke neman hanyar samun waraka daga kaikayin gaba, har ma a wasu lokutan suke fitar da ruwa mai wari, sai su tanadi waɗannan abubuwan kamar haka, 

  • Miski daya, 
  • Zuma kamar cokali biyu,
  • Man zaitun cokali biyu,

Sai su hada su guri daya, a samu ƴar auduga, a goga abubuwan nan da aka hada da zarar an idar da sallar Asuba, sannan a nemi ruwan dumi, a kama ruwa da shi. Sai ki dauki Audugar da ki ka goga wancan hadin a jiki, sai ki tura audugar ciki kadan, ki bar shi har tsawon awa hudu, ko fiye da haka, sai ki cire. Sannan ki kama tsarki da ruwan dumi. Idan kuka yi ta maimatawa, har tsawon sati guda, insha Allah duk wata cuta da warin gaba za su kau. Allah ya sa mu dace.


Yadda ake gyara jiki 

Batun sirrin gyaran jiki, ya kamata mu sani cewa jikin mace na bukatar kulawa a kullum. Ya ke ‘yar’uwa, kina iya samun Lalle, ki jika shi, bayan ya kwana, ki tace ruwan ki zuba Humra da Turare, sai ki yi wanka bayan kin yi wankan, kina iya tafasa Lallen, ki zuba a roba ki zauna a ciki kamar na mai jego, wato ‘Sit bath, ’ ki dan zauna a cikin shi na dan lokaci, wannan sirrinsa shi ne fatar ki ba za ta taba lalacewa ba, kuma kariya ce ga saurin takurewar fata. Yana maganin cututukan gaban mace kuma yana kara tsuke mace. Bayan haka, yana maganin basir da kuma karin ni’ima ga mace.


Akwai wani nau’in sinadari na yadda ake karin ni’ima wanda yake da saurin bayar da sakamakon da ake bukata, wato ‘Sharp-sharp, ’ kamar yadda masu hikima ke cewa. Ki samu danyen Zogale ki hada da Cocumber, ki markada su, sai ki zuba madarar ruwa, ki adana sai ya yi sanyi. Sannan an fi so a rika sha da maraice. Allah ya taimake mu.


Akwai kuma hadin sabulun tsarki da kan ki za ki hada, kun san yin tsarki da sabulun wanka yana kawo wa mace matsala, saboda irin sinadaran Chemicals din da ake hada sabulun yana da hatsari ne ga dan Adam, musamman mata, amma wannan hadin sabulun za ki yi tsarki da shi cikin kwanciyar hankali, ba tare da wata damuwa ba, kuma bayan haka yana maganin cututuka na kaikaiyin gaba, da sauransu.


Da farko, zai ki nemi sabulun Zaitun, amma fa wanda aka rubuta Zaplan a jikin kwalin, kada a ba ki mara kyau. Sai ki nemi Bagaruwa, ki daka ya yi lukwi, ki zuba a roba sai ki yanyanka sabulun zaitun din kanana a kan garin bagaruwan, ki dauko Miskin da kika hada tare ki Kwaba shi da ruwan Hulba, ki kwaba su sosai har sai ya yi kauri. Sai ki zuba a roba mai kyau ki rufe, ko kuma ki samu turmin ki ‘yar karama, ki daka sabulun a ciki. Sai ki rika wanka da abinki, kina tsarki da shi. Kwararru a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa irin wannan Sabulun ba shi da wani hadari ko ‘Side effect’ ga mace, kuma zai kara tsuke mace, sannan ta rika kamshi da ni'ima. 


Shawara gareku mata kan yadda ake inganta lafiyar jiki 

Idan kina da sha'awar hips din ki su kara girma bayan wannan hadin da na fada zaki iya siyan maganin da aka hada kan yadda ake ƙara samun girman hips dan ƙara zaman lafiya a zaman takewar aure.


Bugu da kari ma ba wai matan aure ne kadai zasu iya amfani da kayan gyaran hips ba, ƴan mata da suke shirin aure da zawara ma zasu iya amfani dashi dan gyara. Ba wai sai matan aure ba ko wacce ma zata iya gyara kanta da ingantattun magungunan musulunci wanda aka yarda dasu kuma ba su da illah. Wasu kuma suna tsoron amfani da wasu magungunan amma suna tsoro abunda zaije yadawo ga lafia jiki dan suna ganin ana tura hotuna a kafafen sadawar mata da yawa sunyi amfani da maganin gyaran hips sun sami matsala.


Ƴar uwa shi dai magani kala-kala ne akwai mai kyau akwai marasa kyau. Yawancin wanda ake nunawa cewa ya kawo matsala yawanci na turawa ne ba na musulunchi ba anan nake kira da ƴan uwana mata indai kina son gyaran hips zaki iya yi kuma kada kiyi wani ɗar a ranki, indai kin tabbatar da ingancin magani zaki saya ki yi amfani dashi amma ki tabbatar da na islamic ne bana turawa ba. Allah yasa mu dace ubangiji ya taimake mu Baki ɗaya amin. 



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post