UWA TA Gari |
Sau dayawa waɗaansu samari idan sun tashi neman aure za su shiga nemane ido rufe saboda abubuwa kamar :-
1 Don ya huce tsanani sha'awar sa ga 'ya mace
2 Wasu don kyawun sura da Allah yayita
3 Wasu suna nemanta don nasabar gidan da ta fito da sauransu,
Ya kamata a sani zama da 'ya mace zaman hakuri ne duk tsananin soyayyar da kuke yiwa junanku wata rana sai ta yima aiki na wauta, me zai tafiyar da auren Ku koda an samu saɓani tsakaninku Ku gyara tsananin ba tare da kowa yajiba ?
1 ka dage tun farko wajen rokon Allah ya baka mata tagari.
2 ka dubi wadda take da sanin addini gwargwado
3 ka dubi mai tausayinka wadda komai ka yi mata na godemaka.
4 Gara ka yarda ka auri jahila domin auran jahila ba kaikadai zai shafaba 'ya'yanka zai shafesu, Sai ka duba sauran dabi'unta masu kyau, to sai kaga zanku yadore.
Allah ya bamu mata Na gari ya kuma bamu zaman lafiya AMEEN