Shawara zuwa ga mazan da suke cin mutuncin matansu |
Muna cikin wani yanayi da wasu mazan aure ba su dauki cin mutuncin matansu na aure a matsayin abin kyama ba
Mafi girma a cikin wannan muguwar dabi'ah shine miji yaci mutuncin matarsa a gaban 'ya'yansu
Mu sani cewa kwakwalwar yaro tana da saurin rike abu, kar ka rena kankacin shekarun danka ko 'yarka, idan ka kuskura ka zagi mahafiyarsu ko kaci mutuncinta ko ka daketa a gaban 'ya'yanta Wallahi har su koma ga Allah ba zasu manta ba
Kuma hakan zai sa 'ya'yanka su taso ba zasu ji tausayinka ba, domin suna kallonka a matsayin mutum mugu marar imani wanda yake cin mutuncin mahaifiyarsu
Idan tsufa ya kamaka kana bukatar 'ya'yanka su taimaka maka ba zasu yi ba, domin ka dasa musu wani irin mummunan ciwo a cikin zuciyarsu wanda baya warkewa
Idan ka fahimci wannan kuskuren; to ko fada zaka yiwa matarka akan ta gyara kuskurenta kar kayi a gaban 'ya'yanku, ka bari sai sun tafi makaranta, ko idan kun shiga daki daga kai sai ita
Sannan Allah Madaukakin Sarki ya umarci maza a cikin Al-Qur'ani cewa su mu'amalanci matansu da kyautatawa
Mata hakuri ake yi da su, suna da saurin juyawa ne, idan rashin kirkinsu ya motsa shaidan ma gudunsu yake, don haka kaima kar ka biye mata, fice daga gidan, idan sun dawo hayyacinsu to suna da dadin mu'amala
Allah Ka kara mana hakuri tsakaninmu da mata mutanen mu.
Datti Assalafy