Sau Uku Nake Ganin Mijina Na Zina Da Kanwata — Android Pols

Sau Uku Nake Ganin Mijina Na Zina Da Kanwata
Sau Uku Nake Ganin Mijina Na Zina Da Kanwata 

 

Sau Uku Nake Ganin Mijina Na Zina Da Kanwata  ce ita, uwar mu da uban mu guda. Ba ita take bi mini ba, akwai na miji a tsakaninmu. Sai dai ita tun tana da shekaru 10 take gabana. Shekaru hudu kenan da aure na. Ta dawo gaba na ne tun bayan hadarin mota daya ritsa mahaifina da uwata da kuka kanina data ke bi masa. Daman mu kenan uku iyayen mu suka haifemu.


Ganin babu wanda zai riketa mijina ya kawo shawarar ta dawo gaban mu kawai ta zauna a lokacin mun haifi dan mu. Haka kuwa aka yi. Daga wannan. Lokacin duk wani hidimar karatunta har ma na rayuwar ta shike Yi mata komai. Duk kuwa da babu laifi iyayen mu sun rasu sun bar mana kudi da kuma gidaje da kuma motocin hawa. Amma wannan bai taba tsole masa idanuwa ba .


Bayan da kanwata ta Kai shekaru 18 ne, a lokacin kuma ta shiga jami'a, daga wannan lokacin sai hakayenta da dabi'un ta duk suka sauya. Inda ta shiga shaye, shaye, karatun ma taki tsayawa tayi. Yau ta ballo mana wannan rikicin gobe wancan. A haka muka rabu da duk motoci guda biyar da muka mallaka. Sai dai a she duk lokacin da muka saka motocin a kasuwa mijina yake saye sai daga baya ne ya sanar Dani motocin duk suna nan so yake idan kanwata ta natsu idan za a mata aure tayi amfani da wasu wajen yi mata hidima.


A gaskiya kulawar da mijina yake nunawa kanwata tamkar shi ya haifeta. Haka kuma kusan ya fini nuna damuwarsa akan rashin natsuwar ta. Sai dai kuma abunda na gano daga baya shine ya jefani cikin rudani da kuma rashin sanin matakin da zan dauka. Wannan yasa na yanke shawarar rubutowa ko zan samu shawarar masu karatu.


Sau uku ina ganin mijina yana zina da kanwata, duk kuwa na farkon ba gani na Yi ba. Sako ne take kokarin tura masa sai tayi kuskuren turo mini. Wanda kamin ta ankara har na saurara.


"Sorry tunda ka fita ka barni a hotel banci nake sai yanzu na tashi naga ka kirani. Ga kayan Mustapha (ba sunan gaske bane mun boye) baka wuce masa da shi gida ba ka manta. Kada ka fadawa matarka yau a gidan zan kwana bana son ta sani zan zo gidan amma sai can da daddare".


Wannan shine abunda sakon muryar ya kunsa.


Nayi kamar mintuna 30 Ina tunanin abunda na saurara. Ina tunanin irin kusancin dake tsakanin mijina da Yar uwata. Da kuma irin kauna da soyyayar da yake nuna mana ashe duk ba saboda Allah da annabi yake Yi ba. Har dai na gama wannan tunane tunane wallahi zuciyata taki ta amince dagaske ne. Kawai sai na yanke shawarar bari na gani zata zo din, zai fadamini ko zai Yi shuru. Idan ta zo kwana Kuma mai zai faru. 


Tabbas bai ce mini komai ba, haka nan kuma wajen 10 da rabi na dare sai ga wayanta tana so a bude mata kofa, daman ta saba yin hakan idan nace baza a bude mata ba sai ya nuna bacin ransa yace Ina nake son taje idan ba wanan gidan ba.


Haka ya yiwa masu gadi magana suka bude mata kofa ta shigo. Anan ne naga kayan da take magana na danmu a hannunta.


Bisa al'ada duk inda 8 da rabi tayi nayi barci, idan ma ban kwanta ba to duk abunda nake yi Ina gyanguadi. Don haka ranar ban Yi barci ba har sai dana ga shigowar ta domin na Kara gaskanta abunda na karanta ba zargi ba.


Duk da bana tunanin akwai abunda zasu iya yi a cikin gidan mu, duk da hakan na kasa rumtsawa, amma ita ko mintuna biyar batayi zaune da mu ba ta tahi na shiga dakinta tayi wanka ta dawo taci kayan kwadayin data shigo da shi. Ni dai sai kallonsu nake da ita da mijina. Amma babu wani alamun damuwa a a fuskata.


"Sister (haka take kirana) dazu knga na turo sako na goge ko" take tambaya ta, nace ban kula ba." Ai na turo miki sakon Amma na goge daman Ina so ne na sani ko Yallabai, (haka take kiran mijina) ya karbo kayan yaro idan bai karbo ba naje na karbo sai Kuma ya kirani shi yasa na goge". Nace mata ban ma gani ba. Duk wannan shi mijina yana zaune yana kallon wqni shiri a talabijin bai ce mana komai ba.

Har na soma gyanguadi sai naji tana sallamata zata je ta kwanta. Ta shiga ta barmu a falo dashi. Shima ba a jima ba yace muje mu kwanta. 


Ba ko yaushe muke kwana daki guda, Yana da nasa dakin nima haka, sai idan nayi sha'awa nake zuwa na kwanta a dakinsa. Haka aka yi a wannan daren dakin nasa na shiga. "Yau kuma tare zamu kwana ne? Yake tambaya ta, ina hamma nace maaa e kodai da matsala ne yace babu.


Cikin dare ina farkawa banji motsin mijina ba.


Ina tashi sai naji alamun ruwa yana zuba a bayan daki da yake dakin akwai wajen wanka. Dana ji alamun shine yake ciki kuma kofar dakin namu a kulle yake sai kawai na ja mayafi na kwanta. Jin alamun sumbatu irin na Jima'i yasa ya sake farkawa.na mqtso kofar ban dakin sai na daina jin motsin komai sai zuban ruwa daga shaya. Na taba kofar na jita a rufe. A lokacin ne nayi magana sai ya amsa mini 'zafi ne yayi yawa tamkar babu na'ura a dakin nace bari na zuba ruwa' cikin karfin hali yake magana wanda babu yadda mutum zai zaci mara gaskiya ne shi."ko zaki shigo ne muyi tare? Ina jin hakan sai kawai hankalina ya kwanta nace Masa a fito lafiya.


Har barci ya dukeni, sai naji an bude kofar dakin mu za a fita, Ina bude idanuwa na sai naga kanwata tumbur ya rike mata kugu sunyi sanda ta fita shi Kuma ya ya rufe kofar nan take na tashi nace masa Kai da wacece haka.


Sai yace " a ina kuma' Yaya a Ina ba yanzu na ganka kamar da mutum ba." Gara da kikace kamar, Ina ji mafarki kika yi" nan take ya manna mini hauka yace shi ya duba kofar ne ko ba a kulle taba.


Nan take nima sai na shiga rudani, shi dagaske ne na ganshi da ita ko dai mafarkin na keyi. A haka har barcin ya sake yin awon gaba dani.


Tun daga wannan lokacin ban samu natsauwa ba a gidan mijina. Ga shi kuma babu wanda zai iya yiwa wannan hiran bare na samu natsuwa ko shawara. Daga lokcin

 zargin mijina da kanwata yayi katutu a zuciya ta.


Na shiga kula da ankara game da duk wani motsin su, na hana shi daukanta ko kaita makaranta kamar yadda yake yi ada, ayi kokarin na fadamasa dalili amma na kasa, inda har ya nuna bacin ransa akan bana son halakarshi da kanwata.


Bayan kamar wata guda da faruwar wannan al'amarin, kanwata ta shiga gari kamar yadda ta saba sama da wata sai a waya amma bata zuwa, shima mijin nawa tambayata yake konaji duriyarta sai nace masa sun fi kusa.


Zazzabi ne mai tsanani ya kama yato wajen karfe 10 na dare, a lokacin mijina baya gida, sai kawai na dauki mota yq fita kai yaro asibiti, bayan Ina asibitin ne ma na kirashi na sanar da shi, inda yace mini yana ma kan hanyar komawa gidane amma gashi nan zuwa, nace masa ba sai yazo ba yaje gidan kawai idan akwai matsala zan sanar da shi.


Likitan data duba mu tace za a bamu gado saboda jikin yayi tsanani. Don haka na Kira mijina na sanar dashi hakin da ake ciki. Yace zai Yi wanka yq zo ya ganmu.


Shugowar baban likitan asibitin ne kuma shawara ya sauya, yace ba sai mun kwana ba za a bamu magunguna mu tafi idan abun babu sauki mu dawo da safe.


Na Kira mijina domin na sanar dashi bai dauki wayar ba sau kusan sau biyar, wannan yasa na yanke shawarar komawa gidan kawai.


Wajen karfe 12 ne saura mintuna 15 na dawo, aka bude mini kofar gidan na shiga,. Daga waje Ina hango fitilar talabijin ce kawai take haskawa a folon dakin ta taga guda da labulensa yake dage. Anan nazo na tsaya bayan nayi sallama ba a amsa ba kuma na saka makulli domin na bude kofar da wata makullin a jiki daga ciki.


Na matso kofar tagar domin leke ko zan iya hango mijina sai kawai na hango shi su shi da kanwata akan doguwar kujerar falon ta masa goho yana zina da ita


Anan bakin tagar na samu waje na zauna da yaro a kan kafata Ina ta kuka da tunanin marakin da zan dauka.


Kukan yaron ne ya ankarar dasu naji ana waye ban dai ce komai ba har zuwa bayan mintuna 5 naji an bude kofar.


"Lafiya na ganki kuma bayan kinci an kwantar daku"? Yana magana cikin nuna damuwa. Bance uffan ba na shiga ciki na wuce dakina ita kuka. Har ya shigo ya sameni yana tambayata me nake yiwa kuka "ko yaron ya kamu da rashin lafiyar da bazai warke bana"? Cikin damuwa yake tambaya ta. Kuka kawai nake yi har ita ma kanwar tawa ta shigo suka sakani a gaba da tambaya. Daga karshe dai nace musu jikin yaron ne amma an bamu magani.


Masu karatu har wannan lokacin ban fadawa kowa abunda yake faruwa a gidana ba tsakanin mijina danake matukar kauna da so, da kuma kanwata da ita kadai ta rage mini a rayuwa.


Ganin yanzu haka mijina yayi tafiya sai karshen wannan watan na wannan sabuwar shekarar zai dawo. Ita kuma kanwata satin ta na uku kenan tana kwance a asibiti ana mata aikin kafarta bayan hadarin da tayi da mota nake son na samu shawara daga kareka ko dalibanka yadda zai shawo kan wannan matsalar ba tare da na samu marsala da mijina ba kuma zumunci na da kanwata bai lalace ba.


Ita son mijina duk da wannan cin amanar, kazalika kanwata. Yaya zanyi?

 

(ba ita bace a wannan hoton ba)

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post