Nasiha Ga Amaren Mu Na Watan December |
Akwai abubuwan da ya dace dukkan amare su sani domin zai taimaka musu wajen ƙara inganta zamantakewar auren su. Ga jerin nasihohin kamar haka.
Nasiha Ga Amaren Mu Na Watan December
(1) Amarya ya kamata ki sani cewar. A bangaren hakki, miji yafi uwa da yafi uba girman hakki.
Dole sai da izininsa zaki fita, dole sai da izininsa zaki aikata kowanne abu, dole sai da izininsa zaki yanke wani hukunci.
(2) Amarya ki sani cewar, Kawaye mutane ne da zakiyi zumunci dasu, amma ba koda yaushe ba, tinda a yanzu kin zama matar aure. Sabida haka sai kin rage committement da Kawaye, musamman ma wadda bata da aure.
Wasu kawayen suna lalata aure, ta hanyar zuga ko hada rigima da fitina. Sabida haka anan sai amarya ta kiyaye.
(3) Amarya ki sani cewar. Yan uwan mijinki, yan uwanka ne, idan kikace sai yan uwanki ne kawai mutane, yan uwansa ba mutane bane. To baki so zaman lafiya ba.
(4) idan mai 'yaya Allah ya baki toh ki sani ‘yayan mijinki tamkar yayanki ne. Daga ranar da kika nuna bakya son daya daga cikin yayansa. Tamkar kince bakya son mijinki ne. Ana chanja mace, amma ba’a chanja ‘ya’ya.
(5) Amarya. Kada ki sake koda da wasa ki kai karar mijinki gidanku. Duk abinda yayi miki idan kikayi hakuri zaku daidaita. Matukar dai akwai soyayya a tsakaninku. Yanzu a gidan miji ake yaji ba gidan iyaye ba.
(6) Amarya, kada ki sake ko da wasa ki tafi gidanku YAJI, yaji yana rage martabar Aure da martabar miji a idon iyayenki.
Wani mijin kuma da zarar kin tafi yaji, xai aika miki takarda gidanku. Kinga ba haka aka so ba.
(7) Amarya, idan kina da kishiya, karki dauka cewar wai an kaiki don kuyi fada da ita ne, ba haka bane, kishiya yar uwa ce, ba Abokiyar fada bace. Abokiyar zama ce, itace ma wadda zata fara zuwa wajenki a daidai lokacin da kika nemi taimako, Sabida itace tafi kowa kusanci dake.