Muhimman abubuwan da ya dace mata ku Sani kafin da bayan aure |
Idan Kin Yi Aure To Ki Sani.
Miji farko Jarabawa ne.
A yi mai bauta haramunne.
A sakashi a rai illa ne.
A riƙeshi da kyau Mutumci ne, domin wani ɓangare ne na Gwagwarmayarki in ke Sista ce. Ba rayuwar zaman aure ne zai kaiki gidan wanda ya aureki ba, Bil-Hasalima ba wai Mijin aure ne kika aura ba, abokin tafiya ne a fagen Addini, dan haka dole ne ya zama kin karkatar da Hankalinki ga Yiwa addini hidima, Auren ya zame miki silar samun cikakkiyar damar yin Gwagwarmayar Addini, idan bai zama haka ba. BABU ALKHAIRI A CIKINSA. Amma fa a gun Sister!
Idan ba ki yi Aure ba, to da farko ki sani...
Ba Mijin Aure ne ya kamata ki nema ba, kamata ya yi ki nemi wanda zai Shugabanceki a tafiyar Addinin Allah, wanda zai zame miki Abokin tafiya kuma mai saita ki akan Hadafin Gwagwarmaya, wanda za ki zama mai taimakonsa akan ayyukansa na Addini. Kar ki ƙasƙantar da kanki ga duk wanda bai cancanci ya Ɗalibantar da ke ba.
Wato duk wanda ba zai zama Malami gareki ba to a nawa tunanin bai kamata ki Alaƙantu da shi ba sam. Domin Addini ya na buƙatar Update ne a koda yaushe ga Wanda ya ke yinsa, shi kuma Aure ya na iyakance rayuwar mace ne da abinda wanda take aure ya Alaƙantu da shi, idan ba Addini za ki ma hidima a gidansa ba to kar ki je. Mun zo Duniya ne ba dan mu rayu ba, mun zo ne mu yi aiki mu barta.
Idan kuma baki da Niyyar yin Aure, kuma Iyayenki sun biye miki da abinda kike so (na rashin Aure zuwa wani lokaci) to ke kina cikin hatsarinda ba zai misaltuba, domin yanzu ke Sheɗan zai mayar TERGET ɗinsa! Ki natsu da kyau ki yi taka-tsan-tsan. Za ki yi saurin samun Allah idan kin nemeshi, kuma za ki yi saurin faɗawa fushin Allah idan kin gujeshi. (Wannan wani bayani ne mai zaman kansa, wata kila ya zo a sati mai zuwa).
~Daga Rubutun wacece Sister part 2