Menene Wahalhalun Daren Farko?

Menene Wahalhalun Daren Farko?

Wahalhalun Daren Farko


Ƴan mata da yawa ana tsorata su game da daren farko, da irin halin da suke samun kansu, hakan yasa muke ta yawan samun tambayoyi daga matan da suke dab da yin aure kan shin menene wahalar daren farko? 


Abin da ake nufi da daren farko shine daren da na miji zai tare da matasar sa, ga al'ada a wannan daren ko kuma dare masu biyowa miji yana saduwa da matarsa ta hanyar jima'i. 


Menene tantanin Budurci a daren farko? 

Tantanin budurci yana kecewa kuma jini yana dan zuba, ko mafi yawancin tantanin kalansa yana da huda-huda a jikin sa shine yafi yawa ga ƴan mata idan ya fashe digon jini ne kawai ke diga a hankali, wato baya zubar da jini da yawa. Wani lokacin ma digo ko daya baya zuba domin tana yuwa ya kece ta hanyar yin jima'i  musanmanma idan ya zama mai kamar roba ne wanda idan an dan dannashi sai ya bude idan kuma an daga shi sai ya dawo yadda yake. 


Mutane da dama basu san haka ba. Abinda suke jira a ranar daren farko shine su ga jini yana diga ta farjin matar wanda idan basu ga haka ba to shikenan za su dauka ba budurwa bace daga nan komai na iya faruwa. Abin kuwa ba haka bane ba llale ne tantanin ya kece a jima'in farko ba.


Abin lura a nan shine mafiya yawancin lokuta bayan saduwa farko tantanin budurci yake kecewa daga nan sai ya zama wata yar fatar nama dake liƙe da gefen farji takan yowu yarinyar ta dan ji zafi a wani lokaci, idan an keta tantanin saboda haka ya kamata Amarya ta jurewa wannan zafin idan zafin ya cigaba a kowa ne jima'i bayan na farko ayi hanzari a ga likita don yin bayani.


Idan amarya tayi matukar razana da wannan dan zafin hakan zai kawo kwanjin cinyarta ya takura, idan haka ya faru to saduwa bazata yiwu ba. A irin wannan halin bai kamata ango ya takura sai yayi ta kowa ne hali ba, abinda yakamata yayi shine su ziyarcii likita tare da amaryarsa su yi masa bayani 

ba kamar yadda za su yi zato ba da zaran ango ya keta tantanin budurci shikenan sai a kowane dare yayi ta aiki abin ba haka yake ba domin kuwa akwai wasu yar raunika da suke faruwa a farjin mace, a sakamakon kecewar tantanin budurci wadanda suke bukatar a basu kwanaki domin su warke. 


Bayan saduwar farko kamata yayi a akalla ango ya bawa amaryar kwanaki kamar 5 kafin ya kara saduwa da ita don raunika su warke 

saboda haka kin wannan saurarawar zai kawowa mace ta ji zafi a duk lokacin saduwa wanda zafin zaiyi tasiri a tunaninta yadda zata rika zato ko tana da wani aibu ne da ya banbanta da sauran mata kamar matsatsin farji da sauran su. 


Gaɓoɓin Jima'i 

A  matsayinki na Amarya yana da muhimmanci ki san waɗannan gaɓoɓi domin samarwa Angonki nutsuwa da kwanciyar hankali, haka kema amarya ya kamata kisan haka.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post